--
DA DUMI-DUMI: Gwamna Zulum ya baiwa matasa 152 tallafin Naira Miliya 100

DA DUMI-DUMI: Gwamna Zulum ya baiwa matasa 152 tallafin Naira Miliya 100
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bawa matasa 152 tallafin Naira N100m. Matasan da suka yi watsi da harkar daba a wata Ƙungiya.

Wannan na zuwa ne biyo bayan kammala shirya musu na tsawon wata guda na horo na tsanaki kan harkokin kasuwanci.

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum a ranar Juma’a ya bayar da tallafin Naira miliyan 100 ga wasu matasa 152 da suka yi gyare-gyare wadanda suka kasance fitattun ‘ya’yan wata kungiyar ‘yan daba ta siyasa mai suna ‘ECOMOG’ a Maiduguri.

Zulum ya basu wannan kudi ne domin su ja jari, su samu kasuwanci da zasu rika ciyar da iyalansu, Don samu ingantacciyar rayuwa

0 Response to "DA DUMI-DUMI: Gwamna Zulum ya baiwa matasa 152 tallafin Naira Miliya 100"

Post a Comment