Federal Government Zata Baiwa Mata Yan Kasuwa Rancen kudi Naira Biliyan 75 Ga Mata Yan Kasuwa
Ministar harkokin jin kai da rage radadin talauci, Dr Betta Edu, ta sanar a ranar Talata cewa, gwamnatin tarayya za ta bayar da lamuni marar riba na Naira 50,000 ga mata yan kasuwa guda miliyan daya da tubu dari biyar (1.5) a karkashin shirin bunkasa sana’o’in gwamnati da samar da ayyukan yi.
Wannan yunƙurin na nufin haɓaka jarin su da haɓaka kasuwanci.
Ta bayyana cewa a ranar 17 ga watan Oktoba ne za a kaddamar da asusun mata yan kasuwa na Naira biliyan 75, wanda za a sanya wa suna asusun Iyaloja Found na ‘yan kasuwa mata marassa galihu.
0 Response to "Federal Government Zata Baiwa Mata Yan Kasuwa Rancen kudi Naira Biliyan 75 Ga Mata Yan Kasuwa"
Post a Comment