Zargi: Ana tsaka da Azumi a Kano wani mutum ya rataye kansa a Bishiya
A na zargin wani mutum ɗan kimamin shekaru fiye da 55 ya rataye kansa da Asubahin yau Laraba a jikin wata Bishiyar Darbejiya dake yankin Gaidar makada a karamar hukumar Kumbotso a Kano.
Wasu shaidun gani da Ido sun ce, mutumin sanye da kaya ruwan Madara a jikin reshen bishiyar wuyansa rataye da igiyar ɗinkin buhu da kuma karin wata wayar charjin waya da ake zargin yayi amfani da su wajen rataye kansa.
Wakilinmu Abba Isah Muhammad,ya yi kokarin jin ta bakin Dagacin Ƴan Kusa, Malam Bala Isa, sai dai dagacin ya ce, zuwa yanzu suna Asibiti, sobada haka sai dai nan gaba.
Hakan zalika wakilinmu namu ya tuntubi Rundunar Yansandan Kano, sai dai zuwa yanzu ba ta ce komai ba, game da faruwar lamarin.
0 Response to "Zargi: Ana tsaka da Azumi a Kano wani mutum ya rataye kansa a Bishiya"
Post a Comment