--
Gaskiyar magana kan kama Umma Shehu da Sadiya Haruna Da Hukumar Hizbah tayi

Gaskiyar magana kan kama Umma Shehu da Sadiya Haruna Da Hukumar Hizbah tayi


Rahotanni sun bayyana cewa HISBAH ta Kano ta kama Tauraruwar fina-finan Hausa kuma tallar kayan jiki na mata, Sadiya Haruna.


Ana zarginta da yada batsane kamar yanda Rahoton ya nunar, saidai zuwa yanzu babu cikakken bayani kan kamen nata.


Bayan kamata ne dai sai abokiyar aikinta, Umma Shehu ta fitar da wani Bidiyo da take inkarin kama Sadiya.


Umma ta yi ikirarin akwai masu neman mata a cikin hukumar Hisbah, kuma manyan su ma wanda idan ta fadesu sai an sha mamaki.


Dalilin yasa, wasu Rahotanni ke cewa, Itama Umma Shehu an kamata. Saidai zuwa yanzu babu wata kafa me zaman kanta data tabbatar da hakan.


Source: Hutudole

0 Response to "Gaskiyar magana kan kama Umma Shehu da Sadiya Haruna Da Hukumar Hizbah tayi"

Post a Comment