--
Ankaddamar Sabon Shirin TISSF na 2025: Lamuni Naira Miliyan 10 ga Ma’aikatan Ilimi a Nijeriya - Duba Cikakken Bayani

Ankaddamar Sabon Shirin TISSF na 2025: Lamuni Naira Miliyan 10 ga Ma’aikatan Ilimi a Nijeriya - Duba Cikakken Bayani


Ankaddamar Sabon Shirin TISSF na 2025: Lamuni Naira Miliyan 10 ga Ma’aikatan Ilimi a Nijeriya - Duba Cikakken Bayani

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da shirin bayar da lamuni har naira miliyan 10 ba tare da kuɗin ruwa ba ga ma’aikatan ilimi na gaba da sakandare a faɗin ƙasar nan, domin inganta walwala da kuma karfafa musu wajen ingabta sana’o’in da suke yi.

Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, ne ya sanar da haka a Abuja, inda ya bayyana cewa shirin, wanda ake kira Tertiary Institutions Staff Support Fund (TISSF), a matsayin shirin haɗin gwiwa tsakanin Ma’aikatar Ilimi, TETFund da Bankin Masana’antu (BOI).

Shirin zai tallafa wa ma’aikata wajen samun kuɗiaɗe buƙatun yau da kullum kamar jinya, haya ginin gida, sayen mota, gudanar da sana’o’in gona da ƙananan sana’o’i, da kuma ci gaba da karatu.

Alausa ya ce shirin zai buɗe ƙofofi ga duka ma’aikatan jami’o’i, kwalejojin ilimi, da manyan makarantun fasaha na tarayya da wasu da aka zaɓa na jihohi, matuƙar suna da akalla shekaru biyar kafin ritaya, kuma suna cikin ƙungiyoyin ma’aikata irin su ASUU, NASU, COEASU, da SSANIP. An tsara biyan lamunin cikin shekaru biyar, inda za a gudanar da tsarin a shafin yanar gizo na www.tissf.boi.ng.

Shugaban Bankin Masana’antu, Dakta Olasupo Olusi, ya tabbatar da cewa tsarin zai kasance cikin gaskiya da sauƙi, yayin da shugabannin ƙungiyoyi da cibiyoyin ilimi suka yaba da shirin tare da neman a ci gaba da aiwatar da shi.

0 Response to "Ankaddamar Sabon Shirin TISSF na 2025: Lamuni Naira Miliyan 10 ga Ma’aikatan Ilimi a Nijeriya - Duba Cikakken Bayani"

Post a Comment