--
An hana Kiran Waya Babu Hawa Yanar Gizo ta Internet A duk fadin Jihar Zamfara Ncc ta dakatar Duba Dalili

An hana Kiran Waya Babu Hawa Yanar Gizo ta Internet A duk fadin Jihar Zamfara Ncc ta dakatar Duba Dalili


Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC) ta ba da umarnin rufe layukan sadarwan daukacin kamfanonin waya a Jihar Zamfara.


Umarnin rufe layukan sadarwan ya fara aiki ne ranar Juma’a a wani mataki na ba wa hukumomin tsaro damar gudanar da aikinsu a Jihar Zamfara, wadda matsalar ayyukan ’yan bindiga ta yi kamari.


Sanarwar da NCC ta fitar ta ce, “Ci gaban matsalar tsaro a Jihar Zamfara ya sa dole a rufe layukan sadarwa gaba daya a fadin jihar daga yau Juma’a, 3 ga Satumba, 2021.


“Hakan zai ba wa hukumomin tsaron da suka dace damar yin abin da ya dace domin dawo da tsaro a jihar.


“Saboda haka ake umartar Globacom ya gaggauta rufe duk tashoshin sadarwa da suke a fadin jihar da ma wadanda ke jihohi masu makwabtaka da ita da za a iya amfani da su wurin sadarwa a cikin jihar.”


Sanarwar ta kara da cewa za a rufe layukan sadarwan ne na tsawon mako biyu a karon farko.


Umarnin rufe layukan sadarwa a Jihar Zamfara na zuwa ne kwana biyu baya. ’yan bindiga sun kai hari a wata makarantar sakandare da ke kauyen Kaya a Karamar Hukumar Maradun ta jihar, suka yi awon gaba da dalibai maza da mata sa da 70.


Harin makarantar ya sa Gwamnatin Jihar Zamfara rufe makarantu a fadin jihar, sai abin da hali ya yi.


An kai wa makarantar harin na ranar Laraba ne washegarin da gwamnatin jihar da wasu makwabtanta suka rufe wasu manyan hanyoyi da kasuwannin dabbobi da sauran matakai a wani yunkuri na fatattakar ’yan bindiga.


Matsalar hare-haren ’yan bindiga ta lakume dubban rayuka baya ga asarar duniyoyi masu yawa, baya ga rana al’ummomi da muhallansu.

0 Response to "An hana Kiran Waya Babu Hawa Yanar Gizo ta Internet A duk fadin Jihar Zamfara Ncc ta dakatar Duba Dalili"

Post a Comment