
Babban Albishir ga wadanda suka taba Neman Aikin 'Dan sanda (Nigerian Police Services) har suka rubuta jarabawa ta Computer Based Tests (CBT) a ranar 5 da 6 na watan March shekarar 2024 amma basu kai ga nasaran samun aikin ba, to daga cikinsu za'a diba
Kamar yadda sanarwa yazo, wannan karon babu batun cike takardan neman shiga aikin 'yan sanda saboda karancin lokaci, za'a deba ne daga cikin wadanda suka taba neman shiga aikin har suka rubuta jarabawa na Computer Based Tests (CBT) a ranar 5 da 6 na watan March shekarar 2024 amma basu kai ga nasaran samun aikin ba, to daga cikinsu za'a diba
A yanzu ana bukatar su shiga cikin wannan website din da za'a bude zuwa nan da karfe 12 na ranar yau: https://apply.policerecruitment.gov.ng
Wanda ya ga sunansa sai yayi printing invitation slip zuwa gurin da za'ayi gwajin lafiya wato medical screening a Police Hospitals dake Zonal Headquarters guda 17 a fadin tarayyar Nigeria
Za'a fara medical screening nan da kwanaki hudu wato ranar 26-2-2025 sannan a kammala zuwa ranar 12-3-2025, wanda bai samu yayi ba shikenan ya wuce shi
Ku taimaka wajen isar da wannan sakon saboda ya isa ga 'yan uwa musamman na kauyuka
Allah Ya bawa mai rabo sa'a
Sako daga Kakakin Hukumar 'Yan Sanda ta Kasa Reshen Jihar Ka: PPRO Abdullahi Haruna Kiyawa
0 Response to "Babban Albishir ga wadanda suka taba Neman Aikin 'Dan sanda (Nigerian Police Services) har suka rubuta jarabawa ta Computer Based Tests (CBT) a ranar 5 da 6 na watan March shekarar 2024 amma basu kai ga nasaran samun aikin ba, to daga cikinsu za'a diba"
Post a Comment