--
A soke lefe da kayan daki wallahi mata sunyi yawa Cewar Fauziyya D Suleiman Tayi bayani cikin Bidiyon Nan Mai tayar da hankali

A soke lefe da kayan daki wallahi mata sunyi yawa Cewar Fauziyya D Suleiman Tayi bayani cikin Bidiyon Nan Mai tayar da hankaliShugabar kungiyar Creative Helping Needy Foundation, Fauziyya D Suleiman ta yi bayani akan wasu dalilai da take ganin ya kamata iyaye su yi la’akari da su don soke kayan lefe da kuma kayan daki.


Ta ce ta bayyana hakane domin ganin halin da ake ciki na tashin hankali da talauci da al’ummar Najeriya ke ciki, Fauziyya ta ce iyaye da dama basa iya yiwa ‘ya’yansu mata da za su aurar kayan daki.


Ta ce sakamakon kungiyar da take jagoranta wacce ke bada taimako a kowacce rana, ta ce babu ranar Allah da ba a kiranta a waya a bukaci su bayar da taimako na kudin kayan daki.


Ta ce akwai matar da ta same ta take bayyana mata cewa sau hudu ana kawo kayan auren ‘yarta, amma saboda basu da kayan daki ya sanya tilas gidan angon suke fasa auren.


Ta kara da cewa akwai wacce ita kuma bazawara ce, ta gaya mata sau uku ana kawo kudin aurenta, amma ganin auren yaki yiwuwa wasu daga cikin mazajen har kokarin lalata suke yi da ita, saboda ganin sun riga sun kai kudi.

Fauziyya ta ce ta san cewa kowacce kasa da kabila da irin al’adarta, amma mu a halin yanzu tunda an kai halin da baza a iya kayan dakin ba, kawai a saukakawa kai.


Ta ce maza su ne masu bada kayan lefe, kuma su ma da dama suna kuka akan hakan, saboda haka ta ce ya kamata a hadu a samu masalaha, ma’ana daga lokacin da iyaye suka ga cewa ‘yar su ta kai minzalin aure kuma basu da kudin kayan daki, to su kira iyayen saurayi su yi magana, su bayyana musu halin da ake ciki, in yaso sai suyi magana akan angon ya kawo duk abinda Allah ya hore masa, su kuma iyayen matar su yi amfani da kudin wajen saya mata kayan da suka ga ya dace, daga nan sai a daura aure cikin rufin asiri kowa ya huta.


Ga dai cikakken bidiyon wanda ta wallafa a shafinta na Instagram:0 Response to "A soke lefe da kayan daki wallahi mata sunyi yawa Cewar Fauziyya D Suleiman Tayi bayani cikin Bidiyon Nan Mai tayar da hankali"

Post a Comment