--
Gaskiya ta bayyana akan zargin da akewa jaruma Rahama Sadau na komawa addinin kiristanci

Gaskiya ta bayyana akan zargin da akewa jaruma Rahama Sadau na komawa addinin kiristanciKamar yadda kuka sani Rahama Sadau ficacciyar jaruma ce a masana’antar kannywood da kuma Nollywood wanda ta kasance tana aikata abubuwan da take janyowa kanta maganganu marasa dadi.


Musamman al’adar da jarumar ta dauka wanda ba irin al’adun ‘yayan musulmai bane tana koyi da wasu abokananta wanda sun kasance ba musulmai ba.


Jarumar takan yi shigar kayan da addinin musulinci bai yarda da shi ba sannan kuma ta wallafa su a shafin na sada zumunta Instagram, inda al’umma fadin abubuwa da dama wanda babu dadin ji ga jarumar.


Jaruma Rahama Sadau tayi wata wallafa a shafin ta na Tweeter kamar haka, a lokacin da wani mutumi ya mata tambaya sannan ta mai da masa da amsa cikin gaggawaBayan Rahama Sadau ta wallafa wannan bayanin sai wani matashi yayi mata tambaya da cewa, naji ance kin koma addinin kiristanci shin da gaske ne.


Wannan cece-kucen ya samo asali ne tun bayan bullar wannan labarin a kwanakin baya a lokacin da wani mawakin kasar waje mai suna, Akon, ya kirata domin ya taimaka mata dalilin korarta da akayi daga masana’antar kannywood


Dalilin wannan korarta da akayi daga masana’antar kannywood shine wakar da sukayi tare da mawakin hausa Hiphop wato Classic, inda aka ga jarumar ta rungume shi ta baya.


To wannan al’amarin yasa akayi ta zargin jarumar da komawa addinin kiristanci duba da wadannan abubuwan da take aikatawa, sannan kuma jarumar ta dauki al’adun mutanen kudancin Nageriya abokadanta tana amfani dasu.


Har kawo yanzu jaruma Rahama Sadau bata daina sanya kayan da zasu janyo mata cece-kuce ba domin a yanzu haka ta sake wallafa wasu sabbin hotunan ta a shafin nata na instagram, kamar yadda zaku gani a kasa.


0 Response to "Gaskiya ta bayyana akan zargin da akewa jaruma Rahama Sadau na komawa addinin kiristanci"

Post a Comment