--
Wayoyin Zamani Guda 20 da Bazasuyi Aiki da WhatsApp Ba Harsai Kamfaninsu Ya Sake Musu Zubin Kwakwalwa,  Duba Koda Akwai Irin Taka

Wayoyin Zamani Guda 20 da Bazasuyi Aiki da WhatsApp Ba Harsai Kamfaninsu Ya Sake Musu Zubin Kwakwalwa, Duba Koda Akwai Irin Taka


WhatsApp, shahararriyar manhajar aike da sakonni mallakar Facebook, na sabunta tsarin manhajar saboda haka kamfanin ya sanar da cewa wasu wayoyin iPhone za su bukaci inganta zubin kwakwalwa zuwa babban zubi don ci gaba da tafiya daidai da bukatar WhatsApp. 


Kamar yadda The Guardian ta ruwaito, kamfanin ya bayyana cewa zai toshe ayyukansa ga wasu tsoffin na'urori farawa daga 1 ga Nuwamba. 


Ya lura cewa masu amfani da wayoyi iPhone wadanda suka saya tun kafin 2016 dole ne su inganta zubin kwakwalwar wayoyinsu zuwa akalla iOS 10. 


Haka kuma, Businessinsider bayyana cewa manhajar WhatsApp din za ta dace kadai ne da na'urorin da ke aiki akan zubin kwalkwalwa na KaiOS 2.5.1 ko sama, wadanda suka hada da JioPhone da JioPhone 2. 


Daga rahotannin da ta tattaro, Legit.ng ta hada jerin wayoyin da za su bukaci wannan ingantawa cikin gaggawa kamar haka: 


iPhone 5 iPhone 5C iPhone 5S iPhone 6 iPhone 6 Plus iPhone SE (1st-gen) iPhone 6S iPhone 6S Plus iPhone 7 iPhone 7 Plus iPhone 8 iPhone 8 Plus 


iPhone 8 iPhone 8 Plus iPhone X iPhone XR iPhone XS iPhone XS Max iPhone 11 iPhone 11 Pro iPhone 11 Pro Max iPhone SE (2nd-gen) 

0 Response to "Wayoyin Zamani Guda 20 da Bazasuyi Aiki da WhatsApp Ba Harsai Kamfaninsu Ya Sake Musu Zubin Kwakwalwa, Duba Koda Akwai Irin Taka"

Post a Comment