--
Anfara aurar da 'yan mata a farashi mai sauki a Jihar kano

Anfara aurar da 'yan mata a farashi mai sauki a Jihar kano


Wasu iyayen amarya sun nemi saurayinta da ya biya kudi zambar naira dubu 300,000 a matsayin komai sai a daura musu aure domin saukakawa juna.


Wannan lamari wanda ya faru cikin watan nan a karamar hukumar Dala cikin birnin jihar Kano yaja hankalin mutane da dama inda suke nuna mamakin su wasu kuma suke nuna jin dadin.


Majiyarmu ta tabbatar mana da cewa yarinyar marainiyace kuma yan uwan mahaifinta sune suka yi wannan hukunci, inda suka bukaci saurayin da ba’a baiyyana sunan sa ba ya kawo naira dubu 250,000 na Lefe da kayan Daki da za’ayi.


Sai kuma naira dubu 50,000 a matsayin sadaki domin kowa ya ya Sami sassauci.


Idan zaku iya tunawa dai tsawon wata guda kenan da yin wani kira da wata marubiciya kuma shugabar gidauniyar tallafawa marasa karfi da marayu a jihar Kano Fauziyya D. Suleman tayi akan cewa.


Yakama iyaye suna zaunawa domin fahimtar junansu akan auran yayansu a saukakawa juna domin rage yawan koke-koke na tsalar rashin kayan daki da na Lefe, kuma gwamnati da malamai da masarautuma suna da hakki si shigo ciki.


Inda bayan wannan gwamnatin jihar Kano ta nuna goyan bayanta ga wannan kira ita.

0 Response to "Anfara aurar da 'yan mata a farashi mai sauki a Jihar kano"

Post a Comment