--
Wanda ba'a biya ba, yajira Layi Zaizo Kansa Gwamnatin tarayya tana cigaba da biyan masu cin gajiyar shirin N-power batch c albashin su

Wanda ba'a biya ba, yajira Layi Zaizo Kansa Gwamnatin tarayya tana cigaba da biyan masu cin gajiyar shirin N-power batch c albashin su


Gwamnatin tarayya tana cigaba da biyan masu cin gajiyar shirin N-power batch c albashin su 

Ana yin amfani da Sabar GIFMIS,don gano wadanda suka ci gajiyar shirri N-power Batch A da B ko wani shiri a gwamnatin tarayya kamar ‘yan NYSC, ma’aikatan da ke karkashin Ma’aikatun gwamnatin tarayya, ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya tun bayan da aka mayar da N-power zuwa Ma’aikatar Agajin Gaggawa,da Ci gaban Jama’a ta Tarayya. a shekarar 2020.


Sauran wadanda suka ci gajiyar N-power da ake ganin za a iya gano su a cikin Sabar sun fice ne daga wadanda suka ci gajiyar N-power wadanda suka sake neman aikin kuma suka yi nasara a cikin wadanda suka ci gajiyar Batch C Npower.


Hakan ya nuna cewa gwamnatin tarayya ba zata biya wanda yake aiki a wata hukuma dake gwamnatin tarayya albashin N-power ba idan yana aiki a wata hukuma ba zaa biya shi ba koda an tura shi wurin aiki, ta hanyar amfani da 

Sabar GIFMIS za'a gano wanda ake zargi.



Ana kira da masu cin gajiyar shirin Npower dasu kwantar da hankulan su, kada su firgita sabar GIFMIS da ita ake amfani wurin biya shiyasa biyan kudin ba zai zama lokaci guda ba, dole sai an bi a hankali an tantance wanda suka dace da shiga shirin. 


©Ahmed El-rufai Idris

Kaduna State Zumunta Youth Awareness Forum.

0 Response to "Wanda ba'a biya ba, yajira Layi Zaizo Kansa Gwamnatin tarayya tana cigaba da biyan masu cin gajiyar shirin N-power batch c albashin su"

Post a Comment