--
Allahu Akbar 😭;- Labarin Al'ajabi me dauke da Darussa__Innalillahi wainna ilaihirrajuun

Allahu Akbar 😭;- Labarin Al'ajabi me dauke da Darussa__Innalillahi wainna ilaihirrajuun


 Labarin Al'ajabi mai cike da darrussa....


Wata Likita ce take bada bayanin cewa wannan bawan Allah dattijo, ya kwashe kusan kwana biyu kwance a asibiti baida lafiya, kuma babu wanda yazo duba lafiyarsa. Kwatsam sai su kaga wani abin al'ajabi ya faru, wannan Hazbiya ta shigo har cikin wannan asibiti ta tsaya saman wannan dattijo tsawon minituna sannan ta tashi ta fita. Bayan kwana daya kuma sai wannan Hazbiya ta sake dawo wa ta tsaya saman wannan dattijo tsawon mintuna sai ta tashi ta koma.


Bayan kwana biyu sai aka samu labarin cewa wannan bawan Allah ya kasance yana ciyar da Waɗannan Hazbaye abinci ne a kowace rana ta Allah.


Allahu akbar, hakika wannan al'amari ne na ubangiji bana wannan tsuntsuwa ba. Duk da kasancewar babu taƙaimaiman asibitin da abun ya faru. Amma labari ne mai cike da darussan ɗauka da zai anfanar da al'umma.


Ubangiji Allah ka bamu ikon kyautatawa bayinka da sauran halittunka.


me za ka iya cewa?

0 Response to "Allahu Akbar 😭;- Labarin Al'ajabi me dauke da Darussa__Innalillahi wainna ilaihirrajuun "

Post a Comment