--
Kunji Wata Musifa :- Akwai Tashin Hankali cikin Wannan Lamarin__Innalillahi wainna ilaihirrajuun

Kunji Wata Musifa :- Akwai Tashin Hankali cikin Wannan Lamarin__Innalillahi wainna ilaihirrajuun


 AKWAI ABIN BAN TAUSAYI ACIKIN WANNAN LABARI.

___________________________________________

.

Wani Yaro ne me kimanin shekara 5 Mahaifiyarsa ta Rasu, Sai yaga Kawai Ya Daina ganinta Sai Ya tambayi babanshi yace: Baba ina mama taje? Se baban yace: mamanka tana lahira, Se yaro yace: yaushe zata dawo? Se baban Yayi shiru baice komai ba,

.

Watarana Yaron Yana wasa da abokanenshi

bayan an gama wasa se kowa yace bari yaje

gida gurin mamanshi se yaron yace shima

so yake idan ya girma ya samu kudi yaje Lahira don babanshi yace mamansa tana Lahira, Se daya daga cikin Abokanensa yace: nima Zaka Je dani? Se yaron yace Ehh

.

Watarana Yaron yana makarantar islamiyya

malaminsu yana wa'azi yana cewa 'duk

wanda ya mutu idan yaje lahira bazai dawo ba' Se yaron Ya daga hannu yace malam toh

idan mutun be dawo ba toh me yakeyi acan?

.

Se malamin yace: Lahira gurine inda ake hisabi wa Matattu kuma duk wanda ya mutu baya dawowa,

.

Se yaron yace: idan mutun ya mutu ina ake

kaishi, se malam yace: Makabarta,

.

Se yaron yace: Meyene Mutuwa? Se malam

yace: mutuwa tana Nufin fitar Ruhi daga jikin dan Adam,

.

Se yaro yace: Toh ina Ruhi yake ajikin dan

Adam? Se malam yace kai yaro ka cika

tambaya dayawa, Je ka zauna,

.

Washe Gari bayan Sallar Asuba se yaron Yazo

gurin babanshi yace ina kwana baba ka

tashi lafiya? Baban yace lafiya qalau, Se yaron yace baba Inada tambaya, se Yace toh inajinka Da na meye Tambayarka? Se yaron yace: baba Wai ina Ruhin mamana yake? Se baban yayi shiru............. Can se baban yace: Yaro saurara in baka wani labari Mamanka ta Rasu, Rasuwa kuma idan akayita ba'a dawowa duk wanda aka zarewa Ruhi daga jikinsa bazai rayu ba, lokacin mamanka ne Yayi Shi Yasa Ta rasu, nima idan lokacina yayi Zan mutu na Barka!

.

Sai yaron yace: Toh baba Don ALLAH idan zaka mutu ka gayamun domin nima inaso Na mutu se In rakaka zuwa gurin mamana naji kewarta wllh baba,

.

Sai baban yayi shiru don yaga Alamar Yaronnan.Yanason Mamansa kuma yaga Alamar lallai yaron Yana bukatar ganin mamanshi, se babanshi yace je kashirya kazo muje zan kaika inda mamanka take yanzu, .

.

Sai yaro yaje yayi wanka Yaci kwalliya yana murna zeje gurin mamansa, Dasauri yazo gurin babanshi yace Baba Gani nashirya muje, se baban yakama Hannun yaron

suka fita suna ta tafiya har suka bar Gari

suka shiga daji, suka Isa makabarta, se baban ya nufi Qabarin maman wannan Yaron, Sai

baban yace; Yaro mamanka tana cikin wannan Qasar, Wannan qasar itace Qabari, kuma duk wanda ya mutu a ciki ake sakashi, kuma duk wanda ya mutu baya iya motsi baya iya komai, ahaka za'a kawoshi

anan gurin kuma a binneshi baya iya yin

komai se ikon ALLAH, Se yaro ya fashe da

kuka ya fadi qasa yace: Mamana yanzu itace a cikin wannan Qasa?

.

Sai yace Toh baba wane laifi tayi da ALLAH ya kasheta? Se baban yace kowa haka ze mutu idan lokaci yayi,

.

Suna zaune se ga wasu mutane sunzo da Gawa za'a binneta a cikin Qabari se yaron ya Qura ido yaga duk yanda ake binne mutun, se suka dawo gida, dasuka dawo gida aduk lokacinda yaron yayi Sallah se yace ALLAH Kaji Qan Mamana!,

.

yaron ya tara kudin wasa, irin takardun da yara ke kira kudi yakai wa malaminsu yace malam nabaka wannan kudi ne don kayiwa mamana Addua!

.

Malam yayi shiru...................

yanajin tausayin wannan yaron yace

kabar kudinka zanyiwa mamanka Addua

kyauta, yaro cikin Kuka yace Nagode!

.

Yaro Dan Qarami Kenan, Wanda bai mallaki hankalinshi ba! Ina ga kai kuma dake da Hankali???

.

Ya Allah kajiqan Iyayenmu, Ka Gafarta Musu Zunubansu, Ka Sanya Aljannna itace Makomarsu!   


Don Girman Allah ɗan uwa idan kakaranta katura a groups sabida al'umma su amfana da kai.

0 Response to "Kunji Wata Musifa :- Akwai Tashin Hankali cikin Wannan Lamarin__Innalillahi wainna ilaihirrajuun"

Post a Comment