--
Wayyo Allah :- Kalli Yanda aka kona wani Mutum Wanda Bashida Laifin Komai...Innalillahi wainna ilaihirrajuun

Wayyo Allah :- Kalli Yanda aka kona wani Mutum Wanda Bashida Laifin Komai...Innalillahi wainna ilaihirrajuun


 HAR YANZU, INA ZUBAR DA HAWAYE IDAN NA TUNA YANDA AKA KONA WANNAN MUTUM MARA LAIFI.

Ranar monday ce , da misalin karfe shidda 6:oopm bazan taba mantawa ba .

Ina tsaye ina jiran keke naped:bayan muntashi daga aiki saiga wani mutum dogo, sanye da bakar riga farin wando yayi zanzaro, yasa bakin cover shoe ya daure ,  yatsaya kusa dani , abinda nayi tsammani dai shima jiran abin hawa yake kamar ni.

Can saiga wani keke naped: ya tsaya amma sai wasu suka riga mu shiga nidashi duk bamu samu shiga ba ...

Sai muka dawo baya domin barin kanhanya kasan cewar atsakiyar hanya mai keke-naped din yatsaya.

Daga cikin wayanda sukayi rububin-shiga wannan keke basu samu guri ba , sai kawai mukaji wata dattijuwar mata mai shekaru tsakanin 55 zuwa 60 , tafara ihu onle! Onle!! Kamin kace me .. tazo ta chakumi wannan matashin saurayi dake kusa dani , cewa jama a akawo min taimako barawo yasace min kudi na...

Nan da nan yan agbero dake gurin suka garzayo..

Babu bincike suka fara bugun wannan matashin saurayi , can sai wani daga cikinsu yace a tsaya nayi tunanin taimakonsa zaiyi ashe duk daya: wai makaho yayi dare...

Sai yace mum nawane kudin naki ? Sai mum tace five thousand ; sai suka soma chaje shi abin da yakara bani tausayi shine ..

Yanda suka tattaro guntayen kudi a al jihunsa makes dubu biyar , suka mikawa wannan mata sannan suka hau bugunsa da itace da duwatsu tun yana iya cewa ni ba barawo bane har ya kasa magana allah sarki babu mataimaki ni kuma ina tsoro inkai gudu muwa ace tare muke domin babu wani mai alamar hankali da zai ce ayi aiki da hujja ...

Haka nayi ta zubar da kwalla sukuma suna ta jibgar sa , nan da nan rigarsa ta koma ja ta jike da jini , nan take saiga wani yakawo gudu muwar taya , allah sarki ! Tunda yaga ankawo taya hankalinsa yatashi domin yasan abinda ake nufi konashi za a yi .

Wani yabada shawara akai shi wani kango nan suka jashi cikin wannan kango haka suka sa masa wuta , ina kuka ita kuma wannan data kala masa laifin sata tana ta dariya..

Wuta nataci har ta kusa mutuwa saiga yarinyar wannan mata da gudu tana cewa mum ga five thousand din da zakiyi sayayya kin barshi a gida karki je gurin sayayyar kiga babu , sai nan take ta kwalla ihu! Cewa akawo guduwa akashe wuta ba barawo bane bayan aikin gama ya gama , nikuwa jinake juwa na dibana ...

Ya Allah karaba mu da mugun ji da mugun gani albarkar Annabi S. A W .

INA JAN HANKALIN YAN UWA , MUGUJI YANKE HUKUNCI BATARE DA HUJJA BA DOMIN ZALINCI NE , ALLAH KUMA DA MUKE ROKONSA BAYA AMSAWA AZZALUMI ADDUA .

0 Response to "Wayyo Allah :- Kalli Yanda aka kona wani Mutum Wanda Bashida Laifin Komai...Innalillahi wainna ilaihirrajuun "

Post a Comment