--
Da Dumi-Dumin Sa:- Sanarwa Daga Mai martaba Sarkin Musulmi Kan Ganin Watan Sallah_ Yan Nigeria sufara Duban Wata Ranar Asabar

Da Dumi-Dumin Sa:- Sanarwa Daga Mai martaba Sarkin Musulmi Kan Ganin Watan Sallah_ Yan Nigeria sufara Duban Wata Ranar Asabar


Sarkin Musulmi ya bukaci Musulman Najeriya su fara duba sabon watan Shawwal


Yayin da shekarar 1443 Hijira ke kawo karshe, Fadar Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III ta fitar da wata sanarwar da ke kira ga Musulman Najeriya su fara neman sabon watan Shawwal daga ranar Asabar.



Sanarwar wadda Arc. Zubairu Haruna Usman-Ugwu – wanda shi ne shugaban gudanarwa na hukumar NSCIA – ya sanya wa hannu, ta ce “Kwamitin Ganin Wata na Kasa (NMSC), Sarkin Musulmi ya umarci al’ummah Musulmi a Najeriya su fara duba sabon watan Shawwal daga Asabar 30 ga watan Afrilu 2022, wanda yyayi daidai da 29 ga watan Ramadan, 1443 AH.



Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Idan Musulmai masu daraja suka ga jinjirin watan, sai Mai Alfarma Sarkin Musulmi zai sanar da ranar Lahadi 1 ga watan Mayun 2022 a matsayin ranar 1 ga watan Shawwal kuma ranar Idul Fitr ke nan. Amma, idan ba a ga jinjirin watan ba a wannan ranar, ranar Litinin 2 ga watan Mayun 2022 ta zama ranar Idul Fitr ke nan.


A karshe sanarwar ta ce ana iya tuntubar dukkan jagororin al’umma a dukkan sassan kasa, da mambobin Kwamitin Ganin Wata na Kasa (NMSC), domin a sanar da su sahihan wuraren da aka ga watan Shawwal 1443 AH.

0 Response to "Da Dumi-Dumin Sa:- Sanarwa Daga Mai martaba Sarkin Musulmi Kan Ganin Watan Sallah_ Yan Nigeria sufara Duban Wata Ranar Asabar "

Post a Comment