--
Labari da Dumi-Dumin sa;- Sallah: Ranar Asabar Za a Fara Neman Wata, In Ji Sarkin Musulmi:-BZ GLOBAL SERVICES

Labari da Dumi-Dumin sa;- Sallah: Ranar Asabar Za a Fara Neman Wata, In Ji Sarkin Musulmi:-BZ GLOBAL SERVICES


Sallah: Ranar Asabar Za a Fara Neman Wata, In Ji Sarkin Musulmi


Kwamitin Kolin Harkokin Addinin Musulunci, NSCIA, karkashin Shugbancin Sarkin Musulmi ta umurci yan Najeriya su fara neman jinjirin watan Shawwal yau Asabar bayan faduwar rana



NSCIA ta taya musulmi murnar kammala azumin watan Ramadan ta kuma yi kira ga yan kasuwa su saukaka farashin kayan abinci


Kwamitin Kolin na Musuluncin ta kuma shawarci Gwamnatin Tarayya da kungiyar ASUU su yi sulhu domin a bude makarantu



Kwamitin Kolin Harkokin Addinin Musulunci, NSCIA, karkashin jagorancin Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar ta taya musulmi murnar Sallah Karama da kammala azumin watan Ramadan, rahoton Premium Times.


A cikin sanarwar da Direktan Gudanar Da Ayyuka, Zubairu Usman-Ugwu ya fitar a ranar Juma'a, NSCIA ta umurci musulmi su aiwatar da darrusan da suka koya a ramadan, wanda shine tallafawa marasa karfi.


Ana bikin sallah karama ne a kowanne shekara bayan kammala azumin watan Ramadan a duk fadin duniya.


Sanarwar ta umurci musulmi su fara neman jinjirin watan Shawwal 1443 AH nan take bayan rana ta fadi a ranar 30 ga watan Afrilu, wanda ya yi daidai da ranar 29 ga watan Ramadan.


NSCIA ta yi kira ga al'ummar musulmi kada su kara farashin kayayyakin abinci da tuni ma sunyi tsada a sassan kasar.

0 Response to "Labari da Dumi-Dumin sa;- Sallah: Ranar Asabar Za a Fara Neman Wata, In Ji Sarkin Musulmi:-BZ GLOBAL SERVICES"

Post a Comment