--
Yanzu yanzu: Za'a Gwabza Babban yaki tsakanin Isra’ila Da Hamas Bayan Ramadan

Yanzu yanzu: Za'a Gwabza Babban yaki tsakanin Isra’ila Da Hamas Bayan Ramadan


BABBAR MAGANA_ Kungiyar Gwagwarmaya Ta Hamas Tace: Za’a Fara Babban Yaki Da Isra’ila Bayan Ramadan.

Daya daga cikin shuwagabannin kungiyar Hamas ya bayyana cewa za’a fara yaki babba bayan watan Ramadan, idan har jami’an tsaron gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta ci gaba da ta’asan da take aikawata a birnin Qudus a halin yanzu.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban

kungiyar Hanas Yahyah Sinwar yana fadar haka a wani taro a birnin Gaza a jiya Asabar ya kuma bukaci dukkan dakarun kungiyar su yi shirin shiga yaki babba da yahudawan Isra’ila. bayan watan Ramadan, idan har yahudawan sun ci gaba da keta hurumin masallacin al-Aksa .

A cikin makonnin da suka gabata , sau da dama jami’an tsaron

HKI sun yi ta keta hurumin masallacin al-aqsa, musamman a lokutan bukukuwan yahudawa. Inda suke korar musulmi masu

ibada a cikin masallacin.

Sinwar ya kara da cewa aikin mayakan kungiyar Hamas ne su kare hurumin wurare masu tsarki a kasar Falasdinu da aka mamaye, kuma masallacin al aqsa na daga cikinsu.

-Bin Muhammad

0 Response to "Yanzu yanzu: Za'a Gwabza Babban yaki tsakanin Isra’ila Da Hamas Bayan Ramadan"

Post a Comment