--
Babban Kuskure Ne Namiji yayiwa Mace Waɗannan Abubuwan>>>

Babban Kuskure Ne Namiji yayiwa Mace Waɗannan Abubuwan>>>


Babban Kuskure Ne Namiji yayiwa Mace Waɗannan Abubuwan>>>


Akwai wasu ɗabi'u da halaye na wasu mazan da suke cutar da mata dasu. Wasu mazan kuwa suke zubarwa kansu mutunci dasu. Akwai mazan da suke rasa soyayyar da ake musu saboda su.


Duk namijin da yake son yayi kyakkyawar mu'amala da mace musamman wace yake nema da aure ko wacce ya aura. To ka guji yiwa mata waɗannan abubuwan kamar haka:


(1) Kada Ka Yiwa Mace Alkawarin Da Bazaka Cika Ba. Duk abinda kasan cewa bazakai ba to kada ka furtawa mace cewa zakai mata.


(2) Kada Ka Furtawa Mace Kalmar So Bada gaske kake ba. Idan kasan cewa baka sonta har cikin ranka bai dace ka furta mata kana sonta ba.


(3) Kada Ka Sake Ka Kwatanta Mace Da Wata Muddin Ba Cewa Zakayi Ta Fita Da Wani Abun Ba. Duk mace bata so a nuna mata cewa wata tafita koda kuwa tafita a zahiri.


(4) Kada Ka Dakawa Mace Tsawa. Ita mace abar a lallaɓa ce, duk irin laifin da taimaka bai dace kai mata tsawa ba ko faɗa ba.


(5) Kada Ka Sake Ka Tona Wani Sirrin Da Mace Ta Baka Ko Ta Faɗamaka. Duk mace tana son kasancewa da namiji wanda zai riƙe mata sirrin ta, tare da bata shawarwari.


(6) Duk Munin Mace Kada Kace Mata Mummunace Ita. Duk mace tana son a yaba halittar ta, bai kamata ka furtawa mace cewa batada kyau ba hakan babban kuskure ne.


(7) Kada Ka Ci Amanarta Musamman Da Wata Na Kusa Da Ita. Babban kuskure ne da cin amana kai mu'amala da wata macen ba tare da kasanar da ita ba.


(8) Kada Ka Gwaleta A Cikin Mutane Ko Mata Gyara Na ƙasƙanci. Duk mace ta tsani a kunyata ta a cikin mutane.


(9) Kada Cutar Da Ita Saboda Soyayyar Da take yi Maka. Wani namijin idan ya fuskanci cewa mace tana son sa, to sai yai amfani da wannan damar yaci zarafin ta.


(10) Kada Ka Zama Mai Tsautsauran Ra'ayi Ko Akida Akanta. kulawa da kuma kyautatawa mace shine abinda ya kamata namjji yai.


Mace idan tana yinka, tana yinka ne gaba ɗayanta jini da tsoka. Ranta da mutuwa. Don haka amfani da wannan nakasar kada ya baka damar ka cutar da ita. 


Su mata abin kulawa ne abin tarairaya ne, duk mace tana son namiji da zai nuna damuwar sa akan ta. Kuma mata suna so suji namji da suke tare dashi yana faɗa musu damuwar su hakan yana ƙara musu kwanciyar hankali da nustuwa a zamantakewar rayuwar su. Da fatan maza za su kula sosai.

0 Response to "Babban Kuskure Ne Namiji yayiwa Mace Waɗannan Abubuwan>>>"

Post a Comment