--
Hukumar NCC ta gargaɗi 'yan Najeriya kan ɗaura bidiyo a TikTok

Hukumar NCC ta gargaɗi 'yan Najeriya kan ɗaura bidiyo a TikTok

 



Hukumar kula da kofofin sadarwa ta Najeriya, NCC ta garagdi 'yan Najeriya kan shiga gasar naɗar wani bidiyo da ake ɗaurawa a shafin TikTok, suna cewa ana iya satar bayanan mutanen.


TikTok ya kasance shafi da ke samun gagarumin karɓuwa da haɓɓaka a Najeriya, musamman tsakanin matasa.


Gasar naɗar bidiyon da ake kira 'Invisible Challange' a turance ya kunshi naɗar bidiyon tsiraici sannan a jirkita a shafin ta yada ba za a iya gane mutum ba.


A wata sanarwa, hukumar NCC ta ce ɓata-gari na hawa shafin inda suke ɗaura ire-iren waɗannan bidiyoyi dauke da adireshin da za a latsa domin kwaikwayo ko jirkita hoto ya koma irin nasu.


Sai dai da zaran mutum ya latsa wannan adireshi hakan zai bai wa masu kutse damar tattara bayanan wayoyin mutane, ta hanyar aike sako biros da ake kira WASP ko W4SP mai haɗari.


Hukumar ta ce ta irin wannan hanya ake yiwa duk waɗanda suka shiga wannan gasa kutse da tattare duk wasu bayanansu na sirri da imel.


Sannan wannan biros ɗin a cewar NCC na tattare har da bayanan hotuna da bidiyo da duk wani abu da ke cikin waya.


Da haka ake yi wa 'yan Najeriya gargaɗi kan gujewa irin waɗannan adireshi da kuma yawaita duba wayoyi ko kamfutocinsu da tsaftace manhajarsu a kai-a kai.


Source: BBC HAUSA 

0 Response to "Hukumar NCC ta gargaɗi 'yan Najeriya kan ɗaura bidiyo a TikTok"

Post a Comment