Wata sabuwa: Matasan nijeriya miliyan 2.7 ne ke fama da cutan kanjamau- INJI UNICEF.
Wata sabuwa: Matasan nijeriya miliyan 2.7 ne ke fama da cutan kanjamau- INJI UNICEF.
Asusun kula da yara na majilisan dinkin duniya yace, matasa 310, 000 ne suka kamu da cutan kanjamau a shekaran 2021, wanda ya kawo adadin matasa masu dauke da cutan kanjamau a duniya zuwa milyan 2.7 a bara.
Unicef tace, kusan yara da matasa 110, 000 masu shekaru daga haihuwa zuwa shekara 19 sun mutu sakamakon kamuwa da cutan kanjamau a shekaran 2021.
An bayyana hakane a wata sanarwa don tunawa da AIDS ta duniya a ranan 1 ga watan disamba na 2022.
Unicef tace, cigaban riga kafin cutan kanjamau da kula da yara matasa da mata masu juna biyu ya kusan ja baya a cikin shekaru uku da suka gabata.
Kusan yara da matasa 110.000, 0 zuwa 19 ne suka karu da cutan wanda ya kawo adadin matasan da ke dauke da cutan kanjamau zuwa milyan 2.7.
Hukuman ta bayyana cewa sabbin kamuwa da cututtuka a tsakanin matasa masu shekaru 15 zuwa 19 sun ragu da kashi 40 cikin 100.
Hukuman ta majalisan dinkin duniya tayi gargadin cewa, kawo karshen cutan kanjamau a kananan yara da matasa zaici gaba da zama mafarki mai nisa matukan ba’a magance matsalan rashin daidaito ba.
Rahoto Hajiya Mariya Azare.
SOURCE: ALFIJIR HAUSA
Kushiga Shafinmu Na WhatsApp Domin Samun Sabbin Labarai Akoda Yaushe: https://chat.whatsapp.com/EDLOh4sS1FX38NCnzRqDPJ
Ku sauke Manhajar Application na Wayar Hannu:https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.news
0 Response to " Wata sabuwa: Matasan nijeriya miliyan 2.7 ne ke fama da cutan kanjamau- INJI UNICEF."
Post a Comment