--
Labaran Yau Laraba: 19/07/2023 CE - 01/01/1445AH Ga Takaitattun Labaran Duniyar

Labaran Yau Laraba: 19/07/2023 CE - 01/01/1445AH Ga Takaitattun Labaran Duniyar


Shugaba Tinubu ya dawo gida Najeriya bayan halartan taron AU, a Kenya. 

'Yan bindiga sun halaka Basaraken Nguru da ke ƙaramar hukumar Aboh Mbaise a jihar Imo.

Akalla lauyoyi 60 ne suka garzaya wata babbar kotun tarayya da ke birnin tarayya domin shigar da kara kan hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) saboda kin sakin Emefiele.

Ma'aikatar Noma ta Najeriya ta tabbatar da bullar cutar Anthrax da ake samu a jikin dabbobi a karon farko a kasar.

Gidajen Burkutu a Taraba sun fara yajin aiki saboda tsadar itacen dafa burkutu da Dawa. 

Gwamnatin Anambra ta ce ta ceto wata yarinya mai shekaru 19 da ake zargin wasu maza 6 sun yi wa fyade a garin Anam da ke karamar hukumar Anambra jihar.

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya amince da nadin wasu mutane 3 a matsayin masu taimakawa da kuma ba shi shawarwari. 

Gwamnatin Nijar ta ci tarar kamfanonin wayar sadarwa 4 kudi sama da CFA biliyan 4 sakamakon kasawa wajen inganta ayyukansu a wasu yankuna na kasar.

Pakistan da Iran sun amince su yi musayar bayanan sirri don yakar ta'addanci. 

Iran ta zartar da hukuncin kisa kan mai safarar ƙwayoyi. 

An kwashe yara 1,200 daga sansanin shaƙatawa bayan gobarar daji a ƙasar Girka. 

Mata 45 za su gurfana a kotu saboda zargin zubar da ciki a Iran. 

Ɗan wasan Tottenham, Harry Kane, ba ya son koma wa kungiyar PSG a kakar bana.

A karon farko tun bayan da ya aike da wasikar rashin tsawaita kwantigiransa ga kungiyar PSG, Kylian Mbabbe zai hadu gaba da gaba da shugaban kungiyar PSG, Nasser Al-Khelaifi.

Credit: El-Mustpha.

0 Response to "Labaran Yau Laraba: 19/07/2023 CE - 01/01/1445AH Ga Takaitattun Labaran Duniyar"

Post a Comment