Gamnan jihar Kano Injiniya Alhaji Abba Kabir Yusuf ya cika alkawarin daya dauka na tura yarinya Nana kasar India domin ayi mata aikin Ido
Nana ita da mahaifanta sun ziyarci mai girma gwamna a yau a gidan Gwamnatin jihar Kano inda gwamnan yayi musu rakiya zuwa mota domin tafiya kasar India.
Idan za'a iya tunawa Nana itace yarinyar data ringa kuka a shekarar 2019 kan tana bukar ganin Abba Gida Gida.
Bayan rantsar da shi a matsayin gwamnan kano, Abba Kabir ya ziyarci Gidan su Nana domin dubata dakuma gaishe da iyayan ta wanda a wannan lokacin ya fahimci yarinyar tana fama da matsala Ido anan take ya dau alkawarin daukar nauyin ta zuwa kasar waje domin duba lafiyar idon nata wanda kuma a yau 21 /9/2023 ya cika wannan alkawarin.
~Umar Saleh Zara
0 Response to "Gamnan jihar Kano Injiniya Alhaji Abba Kabir Yusuf ya cika alkawarin daya dauka na tura yarinya Nana kasar India domin ayi mata aikin Ido"
Post a Comment