--
LIKITANCIN ANNABI MUHAMMAD (S) GA MASU SON RAYUWA CIKIN KOSHIN LAFIYA

LIKITANCIN ANNABI MUHAMMAD (S) GA MASU SON RAYUWA CIKIN KOSHIN LAFIYA


RASHIN CIKA CIKI DA ABINCI: Qoshi ko take ciki da abinci, shi ne matakin farko na miqa kai ga kamuwa da cututtuka a jikin dan'adam, domin kaso mafi tsoka na cututtuka suna damfare ne da abincin mutum, da kuma alaqar wasu abubuwa da gangar jikinsa.

Da yawa daga Annabawan Allah, sun koyar da al’ummarsu muhimmancin taqaita qoshi, Annabi Isah (AS) ya cewa Banu-Isra’ila; “Ya ku Banu-Isra’il, kada ku ci abinci har sai kun ji yunwa, kuma idan kun ji yunwa, ku ci, amma kar ku qoshi da yawa, domin kuwa idan kun qoshi, wuyayen ku za su yi nauyi, (wato za ku samu kasalar ibada), jikin ku zai yi teba, sai ku manta da Ubangijinku”. (Wasaa’il, 16-411).

Manzon Allah (S) ya tarbiyyantar da al’ummarsa kan muhimmancin taqaita cin abinci da qaranta qoshi, domin shi ciki burgami ne maqunshin cututtuka. Sarkin daular Qusdandaniyya ya taba aikawa Manzon Allah (S) da kyautar baiwa, da kuma 'kwararren likita don kula da lafiyarsa, sai Manzon Allah (S) ya karbi kyautar baiwar, amma sai ya cewa likitan ya koma, ya ce masa; "Mu mutane ne da ba ma cin abinci sai mun ji yunwa, kuma idan mun ci ba ma cika cikin mu. Ka ga ba mu da buqatar likitan cututtuka kenan".

An ruwaito Manzon Allah (S) yana cewa; “Ka ci (abinci) kana sha’awarsa, kuma ka kame (daga cinsa) kana sha’awarsa”. A wani wuri ya ce; “Da a ce mutane za su riqa taqaitawa a cikin (cin) abinci, to da jikkunan su sun daidaita, (ma’ana da sun samu lafiyar jiki)”. (Wasaa’il, 16-406).

Jikan Manzon Allah (S) Imam Sadiq (AS) ya ce; “Babu makawa ga dan'adam dangane da cin abinda zai wanzar da tsatsonsa da shi, don haka idan dayan ku zai ci (abinci), ya sanyawa sulusin cikinsa abinci, sulusinsa abin sha, sulusinsa kuma (ya bar wa) numfashi, kada ku riqa yin teba (saboda yawan cin abinci), irin tebar aladen yankawa”. (Wasaa’il, 16-406).

Khalifan Manzon Allah (S), Amirul Muminin (AS) ya cewa xansa Imam Hasan (AS); “Shin in sanar da kai abubuwa guda hudu, wanda za ka wadatu da su daga neman magani?” Ya ce; eh (ya Babana), sai ya ce masa; “Ka da ka zauna (cin abinci) face in kana jin yunwa, ka da ka tashi akan abinci face kana sha’awarsa, kuma ka tattauna shi da kyau (kafin ka hadiye), idan za ka kwanta barci ka ziyarci bayan gida. Idan ka riqa aikata haka, to ka wadata daga neman magani”. (Wasaa’il, 16-409).

WANKE HANNU: Hannu shi ne ya fi ko'ina a jikin dan'adam saurin haduwa da 'kwayoyin cututtuka, saboda ya fi kowace gaba yawan aiki na taba abubuwa daban-daban. Wataqil wannan dalilin ne ya sa Manzon Allah (S) ya sunnanta wanke hannuwa kafin cin abinci, da kuma wanke su bayan an kammala cin abincin.

Manzon Allah (S) ya ce; “Wanda ya wanke hannu kafin (cin) abinci da bayansa, zai rayu cikin yalwar arzikinsa, kuma ya waraka daga bala’i (na cututtuka) a cikin jikinsa”. (Wasaa’il, 17-198).

TAUNA ABINCI YA YI LAUSHI: An ruwaito cewa, daga dabi’un Manzon Allah (S), ba ya hadiye abinci da wuri, sai ya dade yana tattauna shi don ya yi laushi sosai, saboda hakan ya taimaka wa qoda wajan sauqin narkar da abinci a cikin cikinsa. Likitoci sun tabbatar da cewa, sinadaran da ke aikin narkar da abinci (emzyms), suna samun sauqin yin aikinsu idan mutum ya tattauna abinci ya yi laushi kafin hadiyewa, kuma suna wahala idan ba a tattauna abincin da kyau ba, dagewa akan yin hakan kuma zai iya haifar da gazawar su wajan aikin narkar da abinci a jikin mutum kamar yadda ya kamata, wanda a qarshe zai iya haifar da cutar nan ta rashin narkewar abinci.

Jikan Manzon Allah (S) Imam Sadiq (AS) yana cewa; “Ku tsawaita zama a akushin abinci, domin shi lokaci ne da ba a lissafa shi a tsawon rayuwarku, ba za a muku lissafi da shi ba”. (Makarimul Akhlaq, shafi na 141).

Ma’ana, ana son cin abinci a natse, kuma a dade ana ci don a riqa tattauna abincin ya yi laushi sosai kafin a hadiye. Domin idan mutum ya zauna cin abinci, to za a dakatar da agogon kusantowar ajalinsa, duk tsawon lokacin da za ka yi kana cin abinci, ba ya cikin lissafin numfashin rayuwarka, sai ka gama sannan agogon ya ci gaba da aiki.

'DANDANA GISHIRI KAFIN CIN ABINCI: A cikin dabi’un Manzon Allah (S) da ya dabi’antu da su, akwai dandana gishiri kafin ya fara cin abinci. Manyan masana ilimin magungunan likitanci na zamani, sun tabbatar da cewa, jikin dan'adam yakan tara wani gwargwado na guba a cikin shekara guda, ta hanyar wasu abinci da abubuwan da mutum yake ci da sha, don haka, dandana gishiri kafin cin abinci shi ne hanya mafi sauri da sauqin kashe 'kwayoyin gubar abincin da mutum zai iya ci a cikin abincinsa a kowane lokaci.

An ruwaito hadisi daga Manzon Allah (S) yana cewa; “Loma uku ta abincin da aka dandani gishiri kafin su, zai turewa dan'adam nau’i 72 na bala’o’i (cututtuka)”.

A wani wuri yana cewa; “Wanda ya lashi gishiri kafin ya ci komai (na abinci), da kuma bayan ya ci, Allah zai tunkude masa nau’i 360 na bala’o’i (cututtuka)”. (Biharul Anwar, 62-293). 

Manzon Allah (S) ya cewa Khalifansa Amirul Muminin (AS); “Ya Aliy, ka bude cin abincinka da (dandana) gishiri, kuma ka rufe shi da (dandana) gishiri, domin duk wanda ya bude (cin) abincinsa da dandana gishiri, ya kuma rufe da dandana shi, za a tunkude masa nau’i saba’in na nau’o’in bala’i (cututtuka), mafi qaranci (a ciki) cutar qurajen qazuwa”. (Wasaa’il, 16-520).

Imam Aliy bin Abiy-Dalib (AS) ya yi wa jama’arsa huduba, ya ce; “Ku fara da (dandanar) gishiri a lokacin cin abincin ku, da a ce mutane sun san abinda ke cikin gishiri (na ‘antibiotic’), da sun zabe shi akan ‘tiryaq’ (Antibiotic) din da aka gwada (aka ga aikinsa)”. (Al-Mahaasin, shafi na 591). (‘Tiryaq’ yana nufin ‘Antibiotic’ ne, sunan wani maganin guba ne mai qarfi a wancan zamanin).

SHAN LEMON TSAMI BAYAN KAMMALA CIN ABINCI. Masana harkar lafiya na zamani sun ce; kyakkyawan abu ne a fagen kula da lafiya, matsa LEMON TSAMI a cikin abinci kafin cin sa, ko kuma shan lemon tsami bayan an gama cin abincin.

Jikan Manzon Allah (S) Imam Sadiq (AS) ya ce; “Ku sha lemon tsami bayan cin abinci, ku sani iyalan Annabi Muhammad (S) haka suke aikatawa”. (Wasaa’il, 17-136).

RIGAKAFI: A sau da yawa mutum yakan samu matsala sakamakon abincin da ya ci, ko wani abin sha da ya sha, domin akan iya cin guba (food poising) a cikin abinci, wanda sakamakon hakan sai mutum ya kamu da ciwon ciki, ko kumburin ciki, ko bacin ciki, ko amai da gudanawa da sauransu. Don daukar matakin rigakafin irin haka, Manzon Allah (S) ya umarci al’ummarsa su tabbatar da tsaftar abinda za su ci, sannan kuma su ambaci sunan Allah a yayin da za su fara ci ko shan duk wani abinci.

Khalifan Manzon Allah (S) Amirul Muminin (AS) yana cewa; “Na lamuncewa wanda ya ambaci sunan Allah akan abinci, cewa ba zai yi kuka da (cin abincin) ba”, (ma’ana ba zai samu matsala da abincin ba). (Hilyatul Muttaqee, shafi na 115).

An ruwaito Manzon Allah (S) yana cewa; “Wanda zai ci wani dan itace (kayan marmari), in ya ce; “BISMILLAHI”, to ba zai cutar da shi ba”. (Makarimul Akhlaq, shafi na 170).

Jikan Manzon Allah (S) Imam Sadiq (AS) yana cewa; “Ku sani, kowane dan itace yana da guba (a jikinsa), idan an kawo muku shi ku tsoma a ruwa ku wanke shi da ruwan (kafin ku ci)”. (Wasaa’il, 17-115).

Khalifan Manzon Allah (S) Imam Baqir (AS) yana cewa; “Wanda yake so kar abinci ya cutar da shi, to ka da ya ci abinci sai in ya na jin yunwa, tumbinsa yana bushe. Kuma idan zai ci, ya ambaci Allah (ya yi Bismillah), kuma ya kyautata tattauna (abincin), sannan ya tsayar da cin abincin a halin yana buqatar sa”. (Wasaa’il, 16-540).

Idan mun lura, wadannan hadisai sun nuna mana matakan kiyaye lafiya har guda shida, rashin cin abinci face in da yunwa, wanke abinda za a ci (idan dan itace ne), yin Bisimilla idan za a ci abinci, markada abincin ta hanyar tattauna shi sosai, da tsayar da cin abinci ba tare da mugun qoshi ba.

CIN KAYAN MARMARI A LOKACINSU: Manzon Allah (S) ya koyar da al’ummarsa cewa su riqa cin kayan marmari a daidai lokacinsu na dabi’a, (wa to a kaka’arsu), domin sun fi amfani a jikin dan'adam a daidai lokacin, ya ce; cin ‘ya’yan itace a lokacin da ba lokacin su ne na dabi’a ba, amfaninsu ragagge ne.

Misali, abubuwan da suke nuna a lokutan sanyi, to an fi so a riqa cin su a lokutan sanyin, a takaita cinsu a lokutan zafi, haka nan abubuwan da suke fitowa a lokutan zafi, an fi so a riqa cinsu a lokutan zafin, a takaita cinsu a lokutan sanyi, domin cin abu ba a lokacinsa na dabi’a ba, yana da tasa fuskar matsala ga lafiya.

An ruwaito Manzon Allah (S) yana cewa; “Na umarce ku da (cin) kayan marmari a lokutan kaka'arsu, domin suna inganta lafiyar jikkuna, su na kawar da damuwa. Amma ku guje su a lokutan da ba nasu ba, domin cuta ne ga jikkuna”. (Xibbun Nabiy (S), shafi na 23).

TSAFTAR MUHALLI: Baya ga tsaftace jiki da abinci, Manzon Allah (S) ya koyar da al’ummarsa tsaftace muhallin da suke rayuwa a cikinsa, domin qazantar muhalli da na kayayyakin mu’amala na yau da kullum, yana janyo cututtuka masu hatsari a rayuwar dan'adam. Kula da lafiya ba kawai kula da jiki da abinci ba ne, ya hada har da kula da muhalli da dukkan abinda ake mu’amala da shi a rayuwa.

An ruwaito jikan Manzon Allah (S) Imam Sadiq (AS) yana cewa; “Ku riqa share farfajiyoyin ku, (farfajiyar gida, ko ta wurin kasuwanci, ko ta wurin zama da sauransu), kada ku kamantu da yahudawa”. (Al-Kaafiy, 06-545).

Imam Baqir (AS) yana cewa; “Sharar gida (ko daki), yana kawar da talauci”. (Al-Kaafiy, 06-545).

Manzon Allah (S) yana cewa; “Gidan shaidanu a cikin gidajenku, shi ne gidan gizogizo”, (ku kawar da shi). (Al-Kaafiy, 06-545).

Imam Baqir (AS) yana cewa; “Kada ku bar yana (yanar datti) a gidajenku, ku kawar da ita da rana, domin ita din mafakar shaidan ce”. (Al-Akhlaqu Wal-Aadab, shafi na 409).

A wani hadisi jikan Manzon Allah (S) Imam Sadiq (AS) yana cewa; “Wanke qore (tukwane da kwanuka da kofuna), yana kawar da talauci (da cututtuka)”. (Wasaal, 15-000).

A wani wuri yana cewa; “Wanke qore da share muhalli, suna janyo arziki”. (Al-Akhlaqu Wal-Aadab, shafi na 409).

A taqaice, wadannan abubuwa guda takwas (8) da muka ambata, sun isa zama misali gare mu na yadda Manzon Allah (S) ya koyar da al’ummarsa matakan kula da lafiya, da gina masu matakan rigakafi masu ingancin gaske. Musulunci addini ne da ke cike da tsafta, da matakan rigakafi na kula da lafiya.

*Assalamu Alaika Yaa Rasulallah*

Daga littafin; "TARIHIN MA'ASUMAI 14 (AS)", Na Adamun Adamawa, wanda zai fito nan gaba kadan insha Allah.

0 Response to "LIKITANCIN ANNABI MUHAMMAD (S) GA MASU SON RAYUWA CIKIN KOSHIN LAFIYA"

Post a Comment