--
An Sake Buɗe Shafin Neman Shiga Shirin SUPA na ITF Kashi na Biyu– Ka Cika Naka Yanzu!

An Sake Buɗe Shafin Neman Shiga Shirin SUPA na ITF Kashi na Biyu– Ka Cika Naka Yanzu!


An Sake Buɗe Shafin Neman Shiga Shirin SUPA na ITF Kashi na Biyu– Ka Cika Naka Yanzu!

Hukumar Industrial Training Fund (ITF) ta sanar da sake buɗe shafin neman shiga shirin Skill-Up Artisans (SUPA) domin baiwa matasa da masu sana'o’in hannu damar samun horo da tallafin kayan aiki ko jari.

Menene SUPA?

Shirin SUPA na da nufin koyar da sabbin dabaru da ƙwarewa ga masu sana’o’i da matasa domin su samu horon zamani a fannoni daban-daban kamar:
- Wanzanci  
- Dinki  
- Gyaran waya  
- Kera kayan aluminium  
- Fenti da sauransu.

 Manufar Shirin:

- Ƙara ƙwarewar sana’a
- Samar da damar samun aiki da rage zaman banza
- Taimakawa wajen samar da kayan aiki ko jari bayan horo

Yadda Ake Cikewa:

1. Ziyarci shafin yanar gizo na SUPA ITF   
2. Cika cikakken bayaninka (sunanka, sana'arka, lambar waya, da sauransu)  
3. Zaɓi fannin sana'a da kake sha'awa  
4. Tabbatar da bayananka kafin turawa.

Ashiga NAN Domin Cikewa

0 Response to "An Sake Buɗe Shafin Neman Shiga Shirin SUPA na ITF Kashi na Biyu– Ka Cika Naka Yanzu!"

Post a Comment