--
Gwagwarmayar Rayuwar Fitacciyar Marubuciya A Yanar Gizo-Gizo (Blogger), Madam Linda Ikeji Daga Shekarar (1980 Zuwa 2023)

Gwagwarmayar Rayuwar Fitacciyar Marubuciya A Yanar Gizo-Gizo (Blogger), Madam Linda Ikeji Daga Shekarar (1980 Zuwa 2023)


DAGÀ Bashir Abdullahi El-bash 

Gwagwarmayar Rayuwar Fitacciyar Marubuciya A Yanar Gizo-Gizo (Blogger), Madam Linda Ikeji Daga Shekarar (1980 Zuwa 2023).

Tun bayan bayyanar fasahar wallafa bayanai a yanar gizo a Nahiyar Afrika, sunan Madam Linda Ikeji na ɗaya daga cikin manyan sunayen manyan marubuta na yanar gizo (Bloggers) da ake ambato. Linda ta yi imanin cewa kafar sadarwa ta yanar gizo (Internet) kafa ce wacce za a iya amfani da ita wajen ƙirƙirar abubuwa da kuma samawa kai daraja har ma da kuɗaɗen shiga.

Linda Ikeji ta kasance marubuciya sannan kuma ƴar kasuwa mai wallafe-wallafe ta hanyar yanar gizo. Ta kasance mace mai wallafa labarai. Sannan kuma jama'a da dama musamman ma matasan ƴan mata su na gamsuwa da ayyukanta tare kuma da samun ƙarfin gwiwar cewa su ma za su iya cimma burukan da su ke da shi a rayuwa.

An dai haifi Linda a ranar 19 ga watan Septemba, 1980 a yankin ƙaramar hukumar Nkwerre a Jihar Imo da ke yankin Kudu maso gabas ɗin Nageriya. Linda ta fara sha'awar wallafa labarai tun ta na ƴar shekara goma da haihuwa a duniya. Kuma ta kasance mai sha'awar aikin Jarida sai dai kuma ta samu nasarar karanta turanci a jami'ar Jihar Legas saɓanin aikin jarida da ta ke da buri.

Linda Ikeji ta samu lambar yabo ta digirin girmamawa a ranar 8 ga watan Ogas, 2018 daga Jami'ar ƙasa da ƙasa ta Trinity da ke ƙasar Geogia a saboda gudunmawar da ta ke bayarwa kan harkokin kafofin watsa labarai da kasuwanci a Nahiyar Afrika.

Kasancewar Linda wacce ta samu kykkyawan horo tun daga tushe a Nageriya, ta fara aiki tun tana ƴar shekara 17 da haihuwa a duniya inda kuma ta ke ɗaukar nauyin buƙatunta da kuma tallafawa iyayenta kuma ta kasance mai matuƙar himma da ƙoƙarin bunƙasa cigaban rayuwarta.

Bayan kammala Jami'a, Linda ta yi aiki tuƙuru inda ta samar da kamfaninta mai zaman kansa kan harkokin aikin jarida mai suna (Black Dove Communications). Inda ta fara buga mujalla mai suna (FM&B Magazine) a shekarar (2006). Kuma waɗannan harkoki nata na (Blogging) ya taimaka mata matuƙa wajen sauya rayuwarta kamar yadda ta bayyana da kanta

Linda ta fara waɗannan harkoki nata na Blogging a shekara ta 2016 tun ma kafin harkokin yanar gizo su yawaita kamar yau a san su, kuma ta na zuwa ne wurin masu kafe ta gudanar da harkokinta a shafinta mai suna (lindaikeji. blogspot. com).

Linda ta shafe tsawon shekaru ta na gudanar da harkokin Blogging ba tare da ta taɓa samun ko sisi ba, amma sannu hankali saboda juriya da jajircewarta yau ta na cikin sahun manyan Bloggers na duniya waɗanda su ka yi nasara kuma su ka shahara. A kullum miliyoyin al'umma ne su ke bibiyar shafin nata domin ganin wallafe-wallafenta.

A ranar 1 ga watan Nobemba, 2006 lokacin da Linda ta ƙaddamar da manhajarta mai suna lindaikejisocial. com sama da mutane 86,000 ne su ka kasance a cikin manhajar cikin ƙasa da kwanaki shida kacal.

Linda ta na da shafinta na Bidiyo mai rabe-raben shirye-shirye iri-iri kamar watsa shirye-shitye kai tsaye da kuma fannin fina-finai ta yadda dukkan masu kallo sai sun biya kafin su kalla ko su sauke fina-finai a wayoyinsu. Sannan kuma bayan TV ta na kuma da gidan Rediyo na kai tsaye Online inda ta ke watsa shirye-shiryenta kai tsaye.

A ranar 5 ga watan May, 2010 Linda ta rubuta littafi na farko kan gamsuwarta da sauyin rayuwar da ta samu. 

Linda a yau ta kasance hamshaƙiyar mai kuɗi a sanadiyyar (Blogging) inda ta sayawa kanta katafaren gida na miliyoyin Naira da kuma Bentley Mulsanne a kan kuɗi ($310,395). Sannan kuma ta na iya biyawakanta dukkan buƙatunta na rayuwa da kuɗaɗen da ta ke samu a wannan harka har ma ta iya tallafawa iyayenta da ƴan uwa da ma dangi da sauran al'umma gaba ɗaya.

Linda ta fidda tsari na musamman kan ayyukan jin ƙai da taimakon al'umma da tallafawa mata matasa masu fiƙirar sana'a da kasuwanci ƴan shekaru 16 zuwa 25 inda ta kashe kuɗi sama da (N10,000,000) a kashin farko na aikin ba da horon tare kuma da alƙawarin cigaba da tallafawa wasu.

A sanadiyyar wannan harka ta (Blogging) Linda ta samu lambobin yabo daga:

BBC a shekarar 2012 da kuma lambar yabo ta shahararrun mata ƴan Afrika (Forbes Africa’s 20 most prominent women, 2012).

Da kuma lambar yabo ta (Nigerian Broadcasters Merit Award (Website / Blog of the Year, 2013).

Sai kuma lambar yabo ta (Nigeria Blog Awards (Best Entertainment Blog)                                      2013).

Da kuma lambar yabo ta babbar mai Bincike a shafin matambayi ba ya ɓata, (Biggest Google search trend in Nigeria                                                  2014).

Da kuma lambar yabo ta ƙasar Amurka ta Duniya kan shugabanci, (United Nations Global Leadership Awards 2018).

Ko shakka babu, lokaci ya yi da sauran matasa musamman na yankin Arewa ya kamata su farka, su fahimci tasiri da muhimmancin kafofin sadarwa na zamani domin su ci ribarta ba wai su tsaya su na ɓatawa kansu lokaci a kan abubuwan da ba za su amfane su ba.

Yanzu dai ga wannan misali na Linda ita dai ba ma'aikaciyar gwamnati ba ce, amma kuɗaɗen da ta ke samu a sanadiyyar (Blogging) sai dai ta yi takarar iya biyawa kai buƙatun rayuwa da ma tallafawa jama'a da manyan ma'aikatan gwamnati ko shugabannin siyasa.

A yanzu da zaka bawa Linda ta wallafa maka wani abu a shafukan ta wata kila idan baka san yadda tsarin yake ba idan kaji kudin guduwa zaka yi.

Duk da cewar a lokacin da ta fara harkar ta (Blogging) ta sha wahala domin ta shafe tsawon shekaru ba tare da ta taɓa samun sisi ba, amma da ta yi haƙuri ta ke kuma yi da gaske yau ga shi ta na cin riba mai girma ta kuma samu ɗaukaka da lambobin yabo a duniya. Dan haka ƙalubale a gare ku matasan Arewa.

Wannan rubutu ne na matasan mu da suke irin wannan bangare na harkar Blogging.

Tarihin Wannan Matar Zai Kara Taimakawa Matasan Mu Na Bloggers Din Mu Na Arewa Su Kara Jajircewa Wajen Gina Media Din Su. 

0 Response to "Gwagwarmayar Rayuwar Fitacciyar Marubuciya A Yanar Gizo-Gizo (Blogger), Madam Linda Ikeji Daga Shekarar (1980 Zuwa 2023)"

Post a Comment