--
Muhimman abubuwa guda biyar da dole sai sun zama daidai  sannan za'ayi nassara wajen  hada Lambar (NIN) Da Layin Waya>>>>

Muhimman abubuwa guda biyar da dole sai sun zama daidai sannan za'ayi nassara wajen hada Lambar (NIN) Da Layin Waya>>>>


Masu bibiyarmu yauma mun sake zo muku da wani sabon tunatarwa game da hada Lambar Shaidar Zama 'Dan Kasa,  wanda akafi sani da (Natinal Identifcation Number) Wato (NIN)


Wanda Gwamnatin tarayya ta sanya doka ga kowanne cikkaken Dan Kasa Daya mallaketa kuma ya hadata da Layinsa Na Wayar Salula, 


To mafiya yawan Al-umma Basusan da Inganci Cewa Abinda Suka Shigar a Layin Nasu Yayi Daidai ba,  Ko Baiyiba, wanda mafiya yawan mutane sun shigar da lambar tasu ta NIN amma har yanzu basu samu sakon tabbacin yayi ko baiyiba,  daga kamfanonin sadarwa na najeriya ba, 


To duk wanda bai samu sakon tabbaciba,  daga kamfanonin sadarwa ba,  Toga Dalilan da suka hana zamu zayyana muku su aqasa domin kowa yaje ya gyara>>>


Muhimmin Abu Na daya: Idan har ya kasance sunan da kake amfami dashi a NIN dinka suna biyu ne ko uku kuma a Rijistar Layinka Na Waya Ba Iri daya Baneba,  To Tabbas Bazai Yiba, 


Muhimmin Abu Na biyu: Idan ya kasance shekarun Haihuwarka Ba Iri daya baneba,  Dana Rijistar Layinka ba,  To shima bazaiyiba, 


Muhimmin Abu Na Uku: Idan Ya Kasance Hoton Yatsun Hannunka Wato (FINGERPRINTS) Idan Shima ya banbanta dana Rijistar Layinka Shima Bazaiyiba,  


Muhimmin Abu Na Hudu: Idan ya kasance Adreshin Gida Daka bayar a NIN dinka ya banbanta dana Rijistar Layinka To Tabbas Shima Ya Zama matsala sosai" 


Muhimmin Abu na Biyar Kuma Na Qarshe Shine: Idan ya kasance hoton mutum dake jikin Rijistar Layin Waya dana NIN ba Iri daya baneba,  To tabbas Shima Matsalace Babba,  


Hanyar Magance wannan matsalar dayace kawai: Shine  Kowa Ya Ziyarci Office Din Kamfanin Layin Sadarwa Kalar Wanda Yake Aiki Dashi Domin ya Sabunta Bayanan Dake Cikin Rijistar Sa,  Kafin nan Da Watan Oktoban Wannan Shakarar>>>


Mungode Kuyada wannan Sakon ga Al-ummah Domin Taimaka musu

0 Response to "Muhimman abubuwa guda biyar da dole sai sun zama daidai sannan za'ayi nassara wajen hada Lambar (NIN) Da Layin Waya>>>>"

Post a Comment