--
Duba yadda Matar aure ta hada baki da kawarta Yar Madigo suka kashe mijinta, duba yadda suka yi

Duba yadda Matar aure ta hada baki da kawarta Yar Madigo suka kashe mijinta, duba yadda suka yi


Yansandan kasar Afrika ta kudu sun kama wata mata mai shekara 26 bisa zargin kasancewa da hannu a kisan mijinta a watan Oktoba na bara a birnin Groblersdal. Shafin labarai na isyaku.com ya wallafa.


Bayan yansanda sun zafafa bincike, daga bisani sun kama wata yar shekara 23 mai suna Patricia Lee Smith, wacce ake zargin cewa yar Madigo ce kuma budurwar matar marigayin. Yansanda sun kama ta ranar 27 ga watan Oktoba 2020, amma suka bayar da ita beli.


Mun samo cewa ranar 9 ga watan Mayu 2020, an yi zargin cewa Yan Madigon sun yi kokarin kashe mijin matar ta hanyar zuba guba a abincinsa. Sai dai an gaggauta kai shi Asibiti inda aka kwantar da shi ya yi jinya har ya warke kuma aka sallame shi.


Sai dai bayan yan watanni, Yar Madigon tare da budurwarta watau matar marigayin suka hada baki duka kashe shi kuma suka batar da gaskiyar lamarin ta hanyar da za a yi zaton cewa an harbe shi da bindiga ne ya mutu sakamakon gaba da hassadar manoma.


Kwamishinan yansanda na Limpopo Lieutenant-General Thembi Hadebe, ya jinjina wa jami'ansa kan namijin kokarin bankado gaskiya dangane da binciken lamari mai sarkakiya kamar wannan.


Yan Madigon za su gurfanar a gaban Kotun Majistare a Groblersdal ranar Juma'a 13 ga watan Agusta, bisa tuhumar kisan kai, hada baki domin a yi kisan kai da kuma mallakan makamin bindiga ba tare da lasisi ko izini ba.


Source: Isyaku.com

0 Response to "Duba yadda Matar aure ta hada baki da kawarta Yar Madigo suka kashe mijinta, duba yadda suka yi"

Post a Comment