--
Kalli Bidiyon Al-ajabi wani mutum da Zakuna suka rungume bayan shekaru 7 da ya ceci rayuwarsu

Kalli Bidiyon Al-ajabi wani mutum da Zakuna suka rungume bayan shekaru 7 da ya ceci rayuwarsu


A kasar South Africa - Wani mutum ya ci karo da Zakunan da ya ceci rayuwarsu a shekaru 7 da suka gabata, haduwar ta baiwa jama'a da yawa mamaki.


Kevin Richardson mamallakin wurin kiwon Zakuna a kasar Afrika ta kudu wanda ya dauka hatsarin haduwa gaba da gaba da Zakunan domin ya tabbatar da cewa ko sun gane shi. 


OMG Newss ta ruwaito cewa Kevin ya taimaka Zakunan yayin da mahaifiyarsu Zakanya ta ki karbarsu a matsayin 'ya'yanta. An gano cewa ya kusanci Zakunan har zuwa inda suke zama kuma ake kula da su. 


Haduwa mai tarin hatsari A wani bidiyon YouTube da Go Pro VR BTS suka nada tare da wallafa shi, Kevin ya ci karo da zakunan masu suna Meg da Ammy a wani rafi kuma gadan-gadan ya nufe su. 


Ya kira sunan daya da ciki yayin da yake matsawa kusa dasu da sauri. A take zakin ya gane wanda ya raine shi kuma ya fada kan shi. Tuni Zakin ya rungume mutumin tare da sumbatarsa. 
0 Response to "Kalli Bidiyon Al-ajabi wani mutum da Zakuna suka rungume bayan shekaru 7 da ya ceci rayuwarsu "

Post a Comment