--
Kalli Hoton dankareriyar motar da mijin Adama Indimi ya gwangwajeta da ita

Kalli Hoton dankareriyar motar da mijin Adama Indimi ya gwangwajeta da ita


Hamshakin mai kudin nan, mijin Adama Indimi kuma yariman Kogi, Malik Ado-Ibrahim ya gwangwaje matarsa da kyautar mota a ranar da suka cika shekara daya da aure. 


Masoyan wadanda suke shagalin cika shekara daya tare a ranar Lahadi, 8 ga watan Augusta sun tafi wani wuri wanda basu bayyana ba don su cigaba da shagalin.


Kanwar Adama, Meram ce ta wallafa hoton kasaitacciyar motar a shafinta na Instagram inda ta rubuta: Na shiga so. Ku kasance a tare har abada InshaAllah 




Hakazalika, shafin 'yan gidansu Adama mai suna @keepingupwiththeindimis ya wallafa a instagram inda suke taya 'yar uwar tasu murnar wannan kyautar girman da aka yi mata. 


A shekarar da ta gabata ne aka yi gagarumin shagalin bikin diyar biloniyan Maiduguri da yarima Malik-Ado Ibrahim. An fara shagalin bikin a Borno kafin daga bisani a koma jihar Kogi inda aka shiryawa amarya Adama gagarumar liyafar cin abincin dare. 


Legit

0 Response to "Kalli Hoton dankareriyar motar da mijin Adama Indimi ya gwangwajeta da ita "

Post a Comment