--
Duba yadda Wani ya yi wuf da jarumar fina-finan 'Kannywood' Diamond Zahra

Duba yadda Wani ya yi wuf da jarumar fina-finan 'Kannywood' Diamond Zahra


Jarumar masana’antar fina-finan Hausa na Kannywood, Zahra Muhammad, wadda aka fi sani da Diamond Zahra ta zama amarya.


Legit Hausa tattaro cewa, jarumar, wadda a yanzu take tashe ta yi aure ne a karshen makon jiya kamar yadda Aminiya ta samu labari. 


Jaruma Bilkisu Abdullahi ce ta bayyana hakan a shafinta na Instagram, inda ta sanya hoton Diamond Zahra din sannan ta ce: 


“Allah Ya ba da zaman lafiya kawata, Allah Ya albarkaci aurenku.” 


Jaruma Diamond Zahra ita ce ke jan fim din ‘Gargada’ wanda Ali Nuhu ya dauki nauyi, sannan tana cikin fim din ‘Farin Wata’ na Adam A. Zango. 


Yanzu haka ana cigaba da daukar shirin na Farin Wata, inda wata majiya ta shaida cewa an musanya jarumar da wata. 


Source: Legit

0 Response to "Duba yadda Wani ya yi wuf da jarumar fina-finan 'Kannywood' Diamond Zahra"

Post a Comment