--
Kalli Hotuna da bidiyoyin liyafar cin abincin dare na auren Yusuf da Zahra, Ali Jita da Breaker sun bajekoli

Kalli Hotuna da bidiyoyin liyafar cin abincin dare na auren Yusuf da Zahra, Ali Jita da Breaker sun bajekoli


Jinin sarauta ne suka hadu da masu mulki a yayin da aka yi liyafar cin abincin dare ta auren Yusuf Buhari da Zahra Bayero Cike da shigar alfarma da kamala aka ga ango,


amarya tare da 'yan uwansu a shagalin da aka yi na ranar Alhamis Mawakan zamani, kuma masu tashe, Ali Jita da Hamisu Breaker Dorayi ne suka nishadantar da wurin da sautikansu 


Kano - Haduwar mulki da sarauta ta matukar kayatar da jama'an da suka halarta da wadanda a hoto suka ga liyafar cin abincin dare na bikin Yusuf Muhammadu Buhari, da namiji daya tilo ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da diyar basarake mai izza, mai martaba, Alhaji Nasir Ado Bayero. 


A ranar Alhamis, 19 ga watan Augusta, wanda yayi daidai da jajiberin daurin auren masoyan biyu ne aka yi kasaitacciyar liyafar cin abincin dare ta bikin 'yan gatan, kamar yadda shafin @thebeginningofyz suka kawo mana. 


Babu shakka amarya Zahra da angonta Yusuf sun matukar yin kyau inda aka ga sun yi shiga ta alfarma cikin wasu kaya masu launin sararin samaniya. 


'Yan uwan amarya sun dauka shigar alfarma cike da kamala a cikin wani yadi mai launin shudi, launin da ya matukar fito da kyawun fatarsu. 


Ba a nan kadai jinin Ado Bayero suka kayatar ba, sun shigo wurin tare da fadawa wadanda ke rike da wata laimar sarauta wacce aka rikewa gimbiya Zahra Nasir Bayero. 




 


'Yan uwan ango sun bayyana a wurin liyafar cike da tasu kalar shigar inda suka shigo tare da wasu masu tsaron lafiyarsu. Babu shakka tsabar mulki ne ke bayyane a tattare dasu. 




Daga cikin mawakan da suka nishadantar da wurin da irin sautinsu da baiwarsu, akwai fitaccen mawaki Ali Jita tare da mawaki mai tashe, Hamisu Breaker Dorayi, wanda ya gwangwaje taron da wakarsa ta Jaruma. 



0 Response to "Kalli Hotuna da bidiyoyin liyafar cin abincin dare na auren Yusuf da Zahra, Ali Jita da Breaker sun bajekoli "

Post a Comment