--
Manyan Labarai: EFCC Ta Kama Tsohon Gwamna A Filin Jirgin Sama Na Abuja, Tinubu Ya Karbi Ziyarar Shettima A London

Manyan Labarai: EFCC Ta Kama Tsohon Gwamna A Filin Jirgin Sama Na Abuja, Tinubu Ya Karbi Ziyarar Shettima A London


EFCC Ta Kama Tsohon Gwamnan Abia A Filin Jirgin Sama Na Abuja


Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati ta kama wani tsohon gwamnan jihar Abia, Sanata Theodore Orji a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe, Abuja.


Kamar yadda Jaridar Puch Ng Suka Wallafa


An kama tsohon gwamnan, wanda ke cikin jerin mutanen da  hukumar, take nema ruwa a jallo,  da misalin karfe 10 na safiyar Ranar Alhamis aka kawo shi hedkwatar EFCC a Jabi, Abuja, don ci gaba da yi masa tambayoyi.


A yanzu haka Orji na cike da alhini tare da dansa, Chinedu, wanda shi ne shugaban majalisar dokokin jihar Abia.


Bola Tinubu Ya Karbi bakuncin Kashim Shettima, Usman Zanna A London


Bola Tinubu, tsohon gwamnan Legas, a ranar Laraba a Landan ya karbi bakuncin tsohon gwamnan Borno, Kashim Shettima.



A halin yanzu Shettima na wakiltar gundumar Borno ta tsakiya a majalisar dokokin kasar.


Honarabul Usman Zanna, wakilin Kaga/Gubio/Magumeri a majalisar wakilai, ya raka Shettima.


Tun a watan Yuli ne shugaban jam'iyyar APC na kasa ya ke Birtaniya.


An sake yi wa Asiwaju wata tiyata kuma yana jinya

0 Response to "Manyan Labarai: EFCC Ta Kama Tsohon Gwamna A Filin Jirgin Sama Na Abuja, Tinubu Ya Karbi Ziyarar Shettima A London "

Post a Comment