--
Kalli Maganar da Rahama Sadau tayi kan shigar amaryar Yusuf Buhari, Zahra Ado Bayero

Kalli Maganar da Rahama Sadau tayi kan shigar amaryar Yusuf Buhari, Zahra Ado Bayero


Biyo bayan kiraye-kiraye da al’umma suka dinga yi a shafukan sadarwa, inda suka yi kira ga mahukunta musamman ma hukumar Hisba akan suyi magana kan shigar da ‘yar Sarkin Bichi Zahra Nasir Ado Bayero tayi a wannan lokaci da ake shirin bikinta da dan gidan shugaban kasa Yusuf Buhari, a karshe dai hukunar ta Hisbah ta fito tayi magana kan wannan lamari.


A wata hira da ya yi da BBC Pidgin, shugaban hukumar Sheikh Haruna Ibn Sina, ya bayyana cewa Zahra ba ta fi karfin doka ba. Inda ya kara da cewa matukar amarya na son aurenta yayi albarka to tilas tayi abinda zai zama abin kwaikwayo ga ‘yan baya.


Haka zalika ya kuma kalubalanci masu yada hotunan amaryar a shafukan sada zumunta, inda ya ce yin hakan zunubi ne a wajen Allah.


Sai dai kuma a wani bangaren, fitacciyar jaruma Rahama Sadau ta mayar da wannan zance sabo, inda tayi wani rubutu a shafin ta wanda ya sanya jama’a suka sake kecewa da cece-kuce a shafinta na Facebook yayin da allura ke neman tono garma.


Ba wani dogon rubutu Rahama Sadau ta yi ba, kawai ta rubuta “RAHAMA SADAU BAIWAR ALLAH“, sannan ta saka alamar gimtse baki, wannan rubutu na ta duk da bata kama sunan kowa ba, sai mabiyanta suka fassara shi da cewar batun auren ‘yar Sarkiin take magana, ma’ana ita tayi shiga irin haka an kusa hhade sama da kasa a kanta, amma ‘yar Sarki tayi irin shigar ba a ce komai ba, akasin nata da Malamai da abokanan sana’arta da al’ummar gari da suka taru suka yi mata rubdugu.



Cikin kwanaki biyu kacal da yin wannan rubutun, amma sama da mutum dubu hudu da dari biyu ne suka yi tsokaci kan rubutun, inda kadan daga ciki sun hada da:


Kiji tsoron Allah kada hangen abinda wasu suka aikata yasakaki shagala shi mahalicci babu ruwansa da kai dan waye. Idan ka aikata alheri shi daka gani idan kuwa ka aikata sabanin sa daka gani. Allah yasa mu dace.


Ayuba Ibrahim

Rahama! Maganarki dutse😋 akasarmu Nigeria indai bakada gata to sunanka sorry 😷 ammafah inkanada galihu to wallahi ko tsirara kake yawo 🧜babu wanda zaicemaka uphan saboda anagudun dauri🚔⚖️🔗gaskiya anji kunya! Allah ya rabamu da son zuciya🏃Up Rahama sadau💪

Dahiru M Sule

Ko kina kokarin halasta kuskurenKi na baya ne bisa ganin wadannan fitsararrun fotunan da suke yawo? Duk sammakal, Kuma ba’a gyara barna da barna. Bada ita zakiyi koyi ba. Da Yar’Gidan Osinbajo zakiyi koyi, wacce ta fito very decent a ranan AurenTa. Ki kiyayi rayuwa‼️

Yusuf Abdullahi Aliyu

 

Matsalar shine ke baki ma fahimci mainene matsalar ki ba har yanzu. Babu wanda ya damu da shigar da kikeyi, in kinga dama ki fito babu kaya ma a jikinki, babu Wanda zai damu da ke, amma dole a damu dake da shigar da kikeyi tunda ta janyo anci mana mutumci an taba mana wanda bamu da kamarsa.


Mukhtar Musa

Da ace Rahama Sadau ce ko wata yar film tayi shigar da Gimbiya zahra yar Sarkin bichi tayi, da yanzu kalmomin kafirci da musgunawa sun cika social media, amma yanzu shiru kake ji, malam ya ci shirwa. Allah ka ganar damu 🙏

Bashir Danrimi


 Source: Labarun Hausa

0 Response to "Kalli Maganar da Rahama Sadau tayi kan shigar amaryar Yusuf Buhari, Zahra Ado Bayero"

Post a Comment