--
Duba dalilan da suka sanya Tsohon Sanata Rochas Okorocha  zai gina Jami'ar Musulumci A Daura>>>

Duba dalilan da suka sanya Tsohon Sanata Rochas Okorocha zai gina Jami'ar Musulumci A Daura>>>


Tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, ya yi alkawarin gina jami’ar addinin musulunci a mahaifar shugaban kasa Muhammadu Buhari. 


Jaridar Premium Times ta ce Sanata Rochas Okorocha ya bayyana cewa gidauniyar nan ta sa, Rochas Okorocha Foundation, za ta yi wannan babban aikin. 


Jigo kuma Sanatan na jam’iyyar APC zai kafa wannan jami’a ne a garin Daura, Arewacin jihar Katsina. 


Menene dalilin kafa jami’ar Musulunci a Daura? Isa Halidu ya wakilci Sanatan na yankin Imo ta yamma, Rochas Okorocha, wajen wani taro da aka yi a Daura, a ranar Asabar, 7 ga watan Agusta, 2021. 


Kamar yadda Halidu ya shaida wa jama’a, ‘daliban wannan jami’a da za a kafa, za su samu ilmi da wurin kwana a kyauta ba tare da sun biya wasu kudi ba. 


“Saboda Mai martaba Sarkin Daura (Umar Farouk Umar) ya ba ni sarautar gargajiya, don haka zan bada tukwuicin da watakila ba za a taba manta wa ba.” 


“Zan gina jami’ar addinin musulunci na zamani a karkashin gidauniyar Rochas Okorocha Foundation, wanda ni da kai na zan kaddamar a garin Daura.” 


Sahara Reporters ta rahoto Okorocha ya na cewa zai yi wannan aiki ne saboda masarautar Daura da daukacin jihar Katsina sun nuna masa soyayya da kauna. Gidauniyar Rochas Okorocha ta saba irin wannan 


A cewar Rochas Okorocha, gidauniyarsa ta gina makarantu da abubuwan more rayuwa a Katsina da sauran jihohi, don haka wannan karo ya zabi garin Daura.


Okorocha wanda ya bar kujerar Gwamna a 2019 ya ce zai yi wannan a mahaifar shugaban kasa saboda kokarin da Muhammadu Buhari yake yi wa Najeriya. 

0 Response to "Duba dalilan da suka sanya Tsohon Sanata Rochas Okorocha zai gina Jami'ar Musulumci A Daura>>>"

Post a Comment