--
Muhimman abubuwa 6 da yasa 'yan mata suke jawa samari aji kafin su amince da soyayyar su

Muhimman abubuwa 6 da yasa 'yan mata suke jawa samari aji kafin su amince da soyayyar su


Kowa dai ya san cewa ‘yan mata a nahiyar Afrika sun yi kaurin suna wajen wahalar da samari, musamman ma idan saurayin shi ya fara nuna cewar yana son budurwar ko da kuwa tana son shi.


Jaridar Yen.com ta kasar Ghana ta bukaci jin ta bakin wasu daga cikin ‘yan matan kasar, da kuma dalilin da ya sanya suke jawa samari aji.


Ga dai amsar da wasu suka bayar a kasa


Wasu ‘yan matan da suke amfani da shafin Facebok sun bayyana ra’ayoyinsu a sashen sharhi, bayan ganin wannan tambaya. jaridar Labarun Hausa ta samo muku kadan daga cikin su.


1. Saboda cin amana da ya faru a baya

Daya daga cikin dalilin shine wadannan matan sun cire rai daga soyayya. Saboda cin amanar da aka yi musu a baya.


Laurene Oumba


2. Don su yi nazari akan saurayin

Saboda mu yi nazari akan saurayin, ba mu son yaudara, yanzu samari da yawa ba abun kirkine yake kai su wajen ‘yammata ba, abinda kawai suke so shine su yaudareki su gudu, saboda haka dole ne mu yi nazari akan saurayin don mu san halayen sa.


Halimatu Sadia AbubakZigaMantey


3. Suna bukatar a wasu su basu dama

Suna bukatar lokaci su tambayi manyan su don su nuna musu hanya, shawarwari da sauran su kafin su amince da soyayyar ka.


Ato Zigaro


4. Suna jira soyayyar saurayin ta shiga ran su

Ba zai yiwu kawai ka yi na’am da soyayyar saurayi ba saboda kawai ya ce yana sonka. Wani lokacin wannan saurayin ya gama karantar budurwar, saboda haka ita maa budurwar tana bukatar lokkaci san ko wanne irin saurayi ne shi.


Wendy MantYvonne


5. Ta kasa jin soyayyarsa a zuciyar ta

Tabbas idan mace tana son saurayi ba ta jimawa tana jan aji, sai dai idan har tana da wasu matsaloli na ta na daban. Lokuta da dama sai kaga ba irin namijin da take son aura bane ko kuma tana shakku akan shi, hakan zai sa dole ta dauki lokaci tana nazarii. Amma abinda nake so mutane su sani shine, duk soyayyar da za tayi karko za ta yi karko ko da kuwa ta jima tana ja masa aji.


Holmes Yvonne


6. Saboda saurayin bashi da kudi

Idan namiji yana da kudi, ko minti daya baza ayi ba za ta amince da shi.


Obaapa Swanzy

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.


Source: Legit.ng

0 Response to "Muhimman abubuwa 6 da yasa 'yan mata suke jawa samari aji kafin su amince da soyayyar su"

Post a Comment