--
Yadda aka kama wani mutum da bindigogi AK-47 53 duba yadda abun ya faru

Yadda aka kama wani mutum da bindigogi AK-47 53 duba yadda abun ya faru


'Yan sanda sun cafke wani matashi a lokacin da yake safarar bindigogi kirar AK-47 guda 53 a Jihar Nasarawa Har ila yau, an kuma gano albarusai akalla guda 260 a wurin mutumin da ya shiga hannu a ranar Asabar, 21 ga watan Agusta Matashin ya shiga hannu ne a hanyarsa ta safarar makaman zuwa wani wuri da ba a sani ba 


Ajihar Nasarawa - Rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa ta cafke wani mutum mai suna Likita Abubakar da makamai. Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an cafke Likita mai shekara 35 dauke da bindigogi 53 kirar AK-47 da harsasai 260, a ranar Asabar, 21 ga watan Agusta.
An tattaro cewa yana shirin kai makaman zuwa wani waje da ba a sani ba a cikin jihar. Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Ramhan Nansel, ya shaida wa Aminiya cewa an cafke wanda ake zargin ne a karamar hukumar Akwanga da ke jihar.

Source: Legit


0 Response to "Yadda aka kama wani mutum da bindigogi AK-47 53 duba yadda abun ya faru"

Post a Comment