--
Yadda akayi Nassarar kashe mesa wadda take hadiye dabbobi Kalli Hotuna

Yadda akayi Nassarar kashe mesa wadda take hadiye dabbobi Kalli Hotuna


A ranar Asabar ɗin da ta gabata ne al'ummar ƙauyen Ilyari da ke arewacin Najeriya suka samu nasarar kashe wata ƙatuwar mesa bayan da aka ganta tana haɗiye wani ɗan akuya a jeji.


Waɗanda suka shaida lamarin sun faɗa wa BBC Hausa hatta dattajai na garin masu shekara 80 sun ce ba su taɓa ganin maciji mai girman wannan mesar ba.


Al'ummar Ilyari, wanda ke ƙarƙashin ƙaramar hukumar Shira a jihar Bauchi da ke arewa maso gabashin Najeriya, sun ce suna zargin mesar ita ce wacce ta daɗe tana haɗiye musu awaki.


Mazauna ƙauyen Ilyari sun ce an shafe tsawon lokaci awakinsu na ɓata kuma sun rasa ina suke shiga.


Sai da wannan lamari ya faru suka gane cewa dama maciji ke haɗiye musu dabbobin idan suka shiga jeji kiwo.


"Awaki da dama muka nema muka rasa a tsawon lokaci ashe maciji ne ke hallaka mana su," kamar yadda wani mazaunin garin ya zarga.


Aliyu Ahmad Ilyari na ɗaya daga cikin waɗanda aka yin gangamin kashe mesar da shi, ya ce yara ne suka ga macijin a ranar Juma'a yayin da suke kiwo a jeji wajen duwatsu.


"Sai kawai suka ga ƙaton maciji ya kama ɗan akuya (taure) wanda a ƙalla ƙuɗinsa zai kai naira 30,000.

"Sai suka gudo gida suka faɗa wa manya, aka je sai aka nemi macijin aka rasa.

"Ya bar wurin kuma lokacin dare ya fara sai aka haƙura aka koma gida," in ji shi.

Malam Aliyu ya ce sai a washe gari Asabar sai aka sake shiri aka bi shi cikin dutsen.

"To a sakamakon nauyin da yake da shi bayan haɗiye tauren duk inda ya bi sai ciyawar wurin ta kwanta, nan aka same shi a kwance.

"An yi masa duka biyu da gora (sanda) sai wani dattijo mai suna Audu Baƙo mai kifi ya kama shi ya yanke kan da wuƙarsa," a cewar Aliyu.

Ganau ɗin ya ƙara da cewa a lokacin da za a ɗauki mesar a kai cikin gari sai da aka tanadi matasa majiya ƙarfi shida.

"Saboda nauyi da kuma tsayinta mutum shidan ma sai da gumi suka kai ta cikin gari. A ƙalla tsayin mesar zai kai tsawon mutum uku," a cewar Ahmad Ilyari.

Bayan an kai macijin gida sai aka yi watandar namansa inda wasu suka dafa suka cinye naman yayin da wasu suka ajiye saboda tarihi a cewar mazauna garin.







Rahoto: bbc hausa

0 Response to "Yadda akayi Nassarar kashe mesa wadda take hadiye dabbobi Kalli Hotuna"

Post a Comment