--
Ana Shafa fatiha ango ya saki amaryarsa bayan samun hotunan tsiraicinta data turawa wani a WhatsApp

Ana Shafa fatiha ango ya saki amaryarsa bayan samun hotunan tsiraicinta data turawa wani a WhatsApp


Wani ango a jihar Kadunan Najeriya, ya yiwa amaryarsa saki ukku ringis a kofar gidansu bayan an gama shafa fatiyar daurin aurensu da ita.


Da wakilansa suka tambayashi dalilin yin hakan sai yace wani tsohon saurayinta ne ya turo masa hotunan ta na batsa wadanda take dauka tana tura masa.


Kuma wanda ya turo ya ce dalilin da ya sa bai sanar da ni kafin a daura aure ba saboda yana fargabar abinda zai biyo baya amma daga karshe ya yanke shawar turo min a ranar daurin auren.


Ni kuma ban samu bude hotunan na gani ba sai bayan an gama daurawa saboda haka na sake ta in ji shi.


Rohoton: APA HAUSA

0 Response to "Ana Shafa fatiha ango ya saki amaryarsa bayan samun hotunan tsiraicinta data turawa wani a WhatsApp"

Post a Comment