--
Amarya ta fasa auren Angonta Ana Tsaka da Biki Ta Fice Daga Gurin Daurin Aure Duba Dalili

Amarya ta fasa auren Angonta Ana Tsaka da Biki Ta Fice Daga Gurin Daurin Aure Duba Dalili


Kowa dai ya san aure biki ne da ake yin shi a bayyanar jama’a domin tabbatarwa da kuma shaidawa tsakanin mutane biyu da suka amince su zauna da juna tare.


Kafin aure, ana bukatar ango da amaryar su samu fuskantar juna sosai kafin su bada goyon baya wajen yin auren su, inda a wasu wuraren ma, iyaye kan shiga cikin lamarin domin gabatar da kwakkwaran bincike akan lamaarin.


Wani abin dariya da ban mamaki da ya faru a wani kauye mai suna Kilifi dake kasar Kenya ya sanya mutane na tofa albarkacin bakin su, bayan amarya ta gudu daga wajen daurin auren su yayin da ta gano cewa mijin ya shirga mata karya.


Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, angon ya bayyanawa amaryar cewa shi ma’aikacin banki ne, hakan ya sanya ta dauki karan so ta dora masa, sai dai kuma lamarin ya canja a wajen daurin auren bayan amaryar ta gano cewa angon da za ta aura ba ma’aikacin banki bane, hasalima shi direban motar haya ne.



Matar mai suna Jackeline Wanjiru ta fito daga cikin cocin da ake daurin auren su ta Mbeeni a lokacin da taji cewa angonta mai suna Alfred Musa, wanda suka shafe shekaru 4 suna soyayya direban motar haya ne, ba kamar yadda ya sanar da ita cewa shi ma’aikacin bankin KCB ba ne.


Rahotannin sun bayyana cewa auren wanda aka yi yunkurin daurawa a ranar Laraba, an dakatar dashi bayan jin wannan abin kunya da ya faru.


Duk kokarin da abokanan ango da ‘yan uwa da abokanan arziki suka yi na ganin sun lallasheta ta koma an daura auren yaki yiwuwa.


To babban darasi dangane da wannan lamari dai shine, mu yi kokari mu zama masu fadar gaskiya a duk inda muka tsinci kan mu. Ku sanar da masoyanku ainahin irin aikin da kuke yi domin su so ku saboda yadda kuke ba wai saboda kudin ku ba.

0 Response to "Amarya ta fasa auren Angonta Ana Tsaka da Biki Ta Fice Daga Gurin Daurin Aure Duba Dalili"

Post a Comment