--
Bayan rasuwar Aisha Dan Kano,  'Yarta Zee Dan Kano Na Neman maye gurbinta Kalli Bidiyon da Zee Dan Kano Keyi

Bayan rasuwar Aisha Dan Kano, 'Yarta Zee Dan Kano Na Neman maye gurbinta Kalli Bidiyon da Zee Dan Kano Keyi


Kamar yadda bayan rasuwar Marigayi Rabilu Musa Ibro, dan sa mai suna Hannafi Rabilu ya daura damarar maye gurbin sa, alamu na nuni da cewa marigayiya Aisha Dan Kano ma za ta iya samun mai gadon ta idan hali ya yi.


A ‘yan kwanakin nan wasu bidiyo suka fara yawo a shafukan Instagram da tiktok na wata matashiya mai tsananin kama da Aisha Dan Kano, wacce ke yin koyi da muryar ta.


Kamannin wannan matashiya mai suna Zee Dan Kano dana marigayiya Aisha Dan Kano ya yi yawa sosai, inda hakan ya sanya ya dauki hankulan al’umma suka dinga mamaki, sai dai kuma bayan bincike da Tashar YouTube ta Tsakar Gida ta yi ta gano cewa Zee diya ce ga marigayiya Aisha Dan Kano. 


Duk da dai Zee ba ta nuna ra’ayi na maye gurbin mahaifiyarta ba alamu na nuni da cewa inda za ta yi hakan za ta bada kwafin mahaifiyarta kwabo da kwabo, sai dai kuma mafi yawan tambayoyin da ake yi mata a shafin ta kan za ta fara fim ne? ba ta bada amsa ba.


Amma tambayoyi da suka shafi dangantakarta da Aisha Dan Kano, ta bada amsa da cewa mahaifiyarta ce, inda mutane da dama suka dinga addu’ar fatan rahama ga mahaifiyarta.


Ga kadan daga cikin bidiyon ta: Ku dannan Link din dake qasa domin kallon bidiyoyin a Tiktok Nata https://www.tiktok.com/@zeedankano



0 Response to "Bayan rasuwar Aisha Dan Kano, 'Yarta Zee Dan Kano Na Neman maye gurbinta Kalli Bidiyon da Zee Dan Kano Keyi "

Post a Comment