--
Zahra Buhari Ta Aike da Sakon Yabo Ga Mijinta Ahmad Indimi Cikin Soyayya da Tsantsar Kauna

Zahra Buhari Ta Aike da Sakon Yabo Ga Mijinta Ahmad Indimi Cikin Soyayya da Tsantsar Kauna


Ɗiyar shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, Zahra Buhari, ta yabawa abokin rayuwarta Ahmad Indimi, cikin soyayya da kauna, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.


Zahra ta yabawa mijin nata ne kasancewarsa abokin rayuwa nagari na tsawon shekarun da suka shafe tare da juna.


Ahmad Indimi, ya garzaya shafinsa na kafar sada zumunta Instagram, inda ya yi rubutu kan nasarar da ya samu wajen zaɓen abokiyar rayuwa,


yace: 

"Nasarar aure na bukatar faɗawa soyayya a lokuta da dama kuma kowane lokaci ina sake faɗawa soyayya da mutum ɗaya." 


Yayin da ya yi wanna rubutun na soyayya ga matarsa, Ahmad ya alakanta rubutunsa da shafin Zahra Buhari. Zahra Buhari ta yaba wa mijinta 


Da take martani kan wannan rubutu, Zahra Buhari tace:


"Ƙa rufe mun baki saboda tsantsar jin daɗi da farin ciki. Tabbas wannan wani ɓangare ne na rayuwar mu, babu matar da takai ni dace da samun miji nagari kamar ka na tsawon shekaru 5." 


Zahra Muhammadu Buhari, da mijinta, Ahmad Indimi, sun yi aure ne a shekarar 2016, shekaru biyar kenan da suka shuɗe. 


Source: Legit

0 Response to "Zahra Buhari Ta Aike da Sakon Yabo Ga Mijinta Ahmad Indimi Cikin Soyayya da Tsantsar Kauna "

Post a Comment