--
'Yan Arewa Mu Farka: Wadanda Basu Cike Abaya Ba, Su Garzaya Ansake bude Shafin NYIF  Suje Su Cike Dan Allah Kuyi Share Zuwa Ga Sauran Mutane

'Yan Arewa Mu Farka: Wadanda Basu Cike Abaya Ba, Su Garzaya Ansake bude Shafin NYIF Suje Su Cike Dan Allah Kuyi Share Zuwa Ga Sauran Mutane



NIGERIA YOUTH INVESTMENT FUND NEW APPLY GA WANDA BASU CIKA BA. 


Asusun saka jarin matasa najeriya NYIF shiri ne da shugaba Buhari ya kawo domin taimaka wa matasa daga kan masu shekaru 18 zuwa 35, domin basu rance su gina kansu, su farfado da sana'o'i. 


Shugaba Buhari ya bayar da Naira biliyan 75 ne akan wannan shirin ta hannun Ministry of Youth And Sports Development, karkashin jagorancin Ministan Sunday Dare.


Idan baku manta ba dai yau kusan tsawon watanin takwas 8 kenan da rufe manjahar neman rancen asusun saka jarin matasa najeriya NYIF yanzu hakan manhajar a bude take wanda basu nema ba zasu iya nema, ku sanar da wanda basu cike ba. 


Duk shekara za'a bayar da Naira biliyan 25 ga matasan Nigeriya, kudin zai kare ne a dai dai lokacin da Baba zai sauka a 2023 in sha Allah.


cikin makon daya gabata in bamu manta ba ma'aikatar matasa da wasanni ta fitar da jarin sunayen mutane 10k wanda zaa turawa gayyatar karbar horo, sai dai har izuwa yanzu 

ma'aikatar matasa bata sanya ranar gayyatar mutane. 


Rubutawa

Comr Abbakar Aliyu Musa AAGwale  National Chairman Zumunta Youth Awareness Forum.


Ga Adreshin Shafin Nan Akasa Aje Acika

https://nyif.nmfb.com.ng/

0 Response to "'Yan Arewa Mu Farka: Wadanda Basu Cike Abaya Ba, Su Garzaya Ansake bude Shafin NYIF Suje Su Cike Dan Allah Kuyi Share Zuwa Ga Sauran Mutane"

Post a Comment