--
Zan siyar da kaina Talaucin Nan Ya Isheni -Cewar Wani Matashi Daga Jihar Kano Kalli Bidiyonsa Yana Bayani

Zan siyar da kaina Talaucin Nan Ya Isheni -Cewar Wani Matashi Daga Jihar Kano Kalli Bidiyonsa Yana Bayani


Wani matashi mai suna Aliyu Idris, ya haddasa cece-kuce a shafukan sada zumunta bayan ya bayyana aniyarsa na son siyar da kansa saboda tsanin da yake ciki na talauci.


A cikin wani bidiyo da shafin Instagram na _garkuwanarewa ya wallafa, an gano matashin dauke da wani kwali a kan titi da rubutun 'Wannan mutumin na siyarwa ne. Ga lambata ga duk mai son siyana, 08140402192.'


Aliyu ya bayyana cewa halin kunci da matsin rayuwa ne ya sanya shi yanke shawarar siyar da kansa. Matashin ya bayyana cewa duk wanda ya siye shi, za su je ayi komai a rubuce sannan a kira yan’uwansa su shaida. sannan ya ajiye lambar wayansa ga duk me ra'ayin siyan nasa. 


A wata hira da aka yi da shi domin sake tabbatar da kudirinsa na son siyar da kansa daga bakinsa, an jiyo matashin na cewa: “Na shirya siyar da kaina indai matukar mutum zai siye ni ba zai yi wani aiki dani da zai saba wa musulunci dani bane. 


Indai matsayin bawa zan tashi a wurin shi, in dai zai bani ci da sha kowane irin aiki ne zan yi masa, zan yi biyayya a gare shi. 


“Na nemi aiki a Kaduna, nan da na zo kano kantin kwari ma na nemi aiki, na nemi dako ban samu ba saboda sun ce ba za su bani dako ba saboda ba a sanni ba ba’a yarda dani ba.” 


Ga bidiyon a kasa: 


0 Response to "Zan siyar da kaina Talaucin Nan Ya Isheni -Cewar Wani Matashi Daga Jihar Kano Kalli Bidiyonsa Yana Bayani"

Post a Comment