--
Dalla dalla: Yadda zaku duba sakamakon  Jarrabawar (NECO) 2021

Dalla dalla: Yadda zaku duba sakamakon Jarrabawar (NECO) 2021


YADDA ZAKA DUBA SAKAMAKON JARRABAWARKA TA NECO


Saukakan matakan da zaku bi domin duba Sakamakon Jarrabawar ku ta NECO sune :


 


•> Da farko za ku shiga Browser din wayarku, Sai ku danna gurin bincike (Search), Sai ku rubuta Adireshin result.neco.gov.ng, Sannan  ku danna Alamar Enter ko kuma Search a Wasu Injinan Binciken


•> Bayan Shafin ya bude zai baku wasu Akwatina guda Hudu, Akwati ta Farko An rubuta Exam Year, Abinda ake bukatar ku sanya a cikin wannan Akwati shi ne Shekarar da kuka rubuta Jarrabawar taku ta NECO Misali 2021,


ii. Sai kuma Akwati ta biyu da zaku ga an rubuta Exam Type, Abinda Ake nufi a wannan Akwatin shi ne wacce irin Jarrabawa kuke son bubawa, Misali SSCE Internal June/July, SSCE External November/December, Basic Education Certificate Examination, ko Kuma Nigerian Common Entrance Examination, To a wannan gidanne zaku saka irin Jarrabawar da kuke son subawa, Misali muce SSCE Internal June/July.


iii. Sai kuma Akwati ta Uku wacce zaku ga An rubuta TOKEN, Abinda ake bukatar ku saka a wannan Akwatin sune Lambobin da kuka saya a Shafin hukumar domin duba Sakamakon Jarrabawar taku, Misali 1630589940, 


iv. Sai kuma Akwati ta Hudu kuma ta karshe a cikin Jerin Akwatunan, Wacce zaku ga an rubuta Registration Number, Abinda Ake bukatar ku saka a wannan Akwatin itace Lambar rijistar Jarrabawarku ta Neco, wacce zaku ganta a jikin katin ku na Jarrabawa (EXAM Card), kuma zaku ga a karshenta da Akwai wasu haruffa guda Biyu.


•> Bayan kun gama Shigar da wadannan bayanan, Abu na karshe da zaku yi shi ne ku danna mabullin CHECK RESULT, wanda zaku ga an rubuta Kuru-Kuru a cikin koren Gida a karkashin wadannan Akwatunan,


    To kuna danna wannan Mabulli na CHECK RESULT, nan da nan Sakamakon Jarrabawar ku na NECO zai bayyana gami da fitowa Dara-Dara a fuskar Waya ko Na'urarku Mai kwakwalwa.


     


Muna tafe da bayani kan yadda ake sayen lambobin duba sakamakon jarrabawar ta NECO na Token Code nan gaba kadan Insha'Allah.


Daga : Miftahu Ahmad Panda (PRO ASOF ONLINE JAMB ORIENTATION COMMITTEE).


    08039411956

0 Response to "Dalla dalla: Yadda zaku duba sakamakon Jarrabawar (NECO) 2021"

Post a Comment