--
Labari mai dadi: Duk wanda yasan ya cike duk wani tallafi N-power, NYIF, Nirsal, Seifac, da sauransu na Gwamnatin Tarayya ya duba wannan Sabuwar Sanarwar

Labari mai dadi: Duk wanda yasan ya cike duk wani tallafi N-power, NYIF, Nirsal, Seifac, da sauransu na Gwamnatin Tarayya ya duba wannan Sabuwar Sanarwar


GA WASU LABARAI MASU DADIN JI HAR GUDA TAKWAS ( 8). AMMA GA MUTANAN DA SUKE CIKE CIKEN DOMIN SAMUN TALLAFI KO BASHI DAGA GWAMNATIN TARAYYA.


1 Ranar 26 ga Watan da Muke ciki ake sa ran Fara biyan ma'aikata na N-Power.


2 Ana GAF da KAMMALA karbar asusun bayanan mutane Wanda Suka cike tsarin RRR Code Kuma kowanne lokaci daga yanzu Wadanda Suka rabauta da Shirin zasu Fara ganin kudade a asusunsu.


3 Nan Kusa acikin Wannan wata ake sa ran  fito da sababbin tsare tsare  domin tallafawa mutanan Kasa ciki harda Wadanda Basu da Account


4 Mutanan da su kaga sunansu a shortlist da aka fitar na  NYIF su Fara Shirin ganin sakon training kowanne lokaci daga yanzu a email dinsu kafin ganin kudade acikin asusunsu da suka bayar, Kuma za'a Kara sakin sunan mutane nagaba.


5 Matsalar Wadanda akayiwa approval Amma kayansu Basu karaso gare suba a tsarin Covid 19 matsalar tazo Karshe ko nace tana GAF da zuwa.


6 Wadanda Suka Shiga Shirin SPW Kuma Suka amfana da Shirin suna GAF da jin matsayinsu akan cigaba da Basu kudi ko dakatar da Shirin Haka.


7 Wadanda Suka Sami kyautar CAC DAGA gwamnatin tarayya shekarar data gabata za'a fito musu da wani tsari Wanda za'a tallafa musu domin Kara rike kansu da sana'arsu, Adadin mutanan shine dubu dari biyu da hamsin Kuma iya su kadai za'ayiwa.


8 Shirin bada tallafin noma da aka Fara bawa mutane zai cigaba Kuma mutane million biyu za'a sake bawa wannan tallafi.


Dukkan Wadannan shirye shirye suna KARKASHIN gwamnatin tarayya Kuma itace take YINSU, Dan Haka mu roki Allah ya tabbatar  da wadannan Abubuwa Kamar yadda aka ambata.

0 Response to "Labari mai dadi: Duk wanda yasan ya cike duk wani tallafi N-power, NYIF, Nirsal, Seifac, da sauransu na Gwamnatin Tarayya ya duba wannan Sabuwar Sanarwar "

Post a Comment