--
Mata ga Naku: Yadda Zaki maida gashin kanki Tamkar Na Indiyawa Ko Larabawa Ta Hanyar Amfani Da Abubuwa Biyu

Mata ga Naku: Yadda Zaki maida gashin kanki Tamkar Na Indiyawa Ko Larabawa Ta Hanyar Amfani Da Abubuwa Biyu


Idan ba ku san yadda ake amfani da man zaitun da tafarnuwa domin kula da gashi ba, to kayanku ya tsinke a gindin kaba.


Hadin man zaitun da tafarnuwa yana da matukar amfani, saboda yana dauke da sinadaren da ke kara wa gashi koshin lafiya. 


Yana kara wa gashi tsayi da cika, ya hana  bushewa ko zubewar gashi, sannan ya kawar da amosanin kai, ya sa gashi laushi, ya kara wa matsirar gashi karfi.


Shi ya sa muka kawo muku yadda ake yin hadin da kuma yadda ake amfani da shi.



Amfanin man zaitun ga gashi:


Kwabin man zaitun da tafarnuwa na dauke da muhimman sinadaran da gashi ke bukata, irinsu selenium, bitamin C, omega 3, omega 6, antimicrobials, oleic acid, kitse, mai da ba shi da karfi, sulfur, antioxidants, bitamin E, bitamin K.


Hadin tsawon gashi:


Idan gashinki mai zubewa ne ko kakkaryewa, sai ki yi amfani da hadin tafarnuwa da man zaitun domin ki jefi tsuntsu biyu da dutse daya — Tsawon gashi da kuma maganin zubewar gashi.


Wadanda kuma tsayin gashi kawai suke bukata, to hakarsu ta cimma ruwa domin zai share musu hawaye, kuma sakamakon da za su samu zai fi kayatarwa.


 


Kayan hadi:


Man zaitun cokali uku

Man ridi cokali uku

Tafarnuwa sala uku

Man tafarnuwa cokali daya (ga mai bukata)

Man Castor oil cokali biyu

Man almonds cokali biyu

Man Rosemary oil cokali daya.

 


Yadda ake yi:


A hada man gaba daya a wuri daya, a nika tafarnuwar sosai a sa a ciki, a bar hadin ya yi kwana hudu.

A rika amfanin da kwabin a lullube gashi, sai a sa tawul mai zafi a rufe a bar shi na tsawon awa biyu.

Daga nan sai a ruwa mai dumi a shamfo da conditioner a wanke.


Daga nan sai a ruwa mai dumi a shamfo da conditioner a wanke.

A maimaita hakan sau biyu a mako daya.

 


Hadin gyaran gashi:


Ga hanyar da za a bi domin samun sakamako mafi sauri na amfani da man zaitun da tafarnuwa don gyaran gashi:


Kayan hadi:


Tafarnunwa sala hudu

Man zaitun kwatan kofi

Man ‘lavender’ (ga mai bukata).

 


Yadda ake hadawa:


A hada man a wuri daya, ita kuma tafarnuwar a nika ta.

Sai a hada man da tafarnuwar a dora a wuta, idan ya yi dumi sai a sauke.

Bayan kwana uku sai a sa a kwalba a rika amfani da shi.


Yadda ake amfani da shi:


A shafa adadin man da ake bukata a gashi a muttsika sosai.

Sai a sa hular gyaran gashi ta leda rufe kan.

Daga nan sai a dora tawul mai dumi a sama.

Bayan kamar awa hudu sai a sa ruwan dumi da shamfo da conditioner a wanke gashin.

Sai a sa wa kan ruwan fure (Rose Water) domin kamshi da kawar da wurin tafarnuwa.

A rika yi sau biyu a mako, za a ga yadda gashin zai sauya.

0 Response to "Mata ga Naku: Yadda Zaki maida gashin kanki Tamkar Na Indiyawa Ko Larabawa Ta Hanyar Amfani Da Abubuwa Biyu"

Post a Comment