--
Neman Aikin 'Yan Sanda Hukumar ta Saki Sabuwar Sanarwa

Neman Aikin 'Yan Sanda Hukumar ta Saki Sabuwar Sanarwa



Rundunar ‘yan sandan Najeriya tare da hadin gwiwar Police Service Commission za su kammala aikin daukar ma’aikatan ‘Yan Sanda dubu goma (10,000) da za a dauka a shekarar 2020.


Sakamakon haka, ana buƙatar 'wanda suka nuna sha'awar su na neman aikin yan sanda su duba matsayin su a tashar daukar ma'aikata, www.policerecruitment.gov.ng wanda za a buɗe daga Litinin, 18 zuwa Talata, 26 ga Oktoba, 2021.



wanda suka cancanci shiga mataki na gaba zasu gudanar da jarrabawa dole ne a gabatar a ranar jarabawar da aka shirya ranar Juma'a, 29 da Asabar, 30 ga Oktoba, 2021 a cibiyoyin da aka keɓe a duk faɗin ƙasar nan. Haka kuma an shawarci masu nema da su duba imel da lambobin waya don sanarwa


Rundunar yan sanda ta ce daukar ma'aikata kyauta ne kuma ba tare an biya wani ko sisi ba ta umarci wanda suka nuna sha'awar su 'da su kira 08100004507 don karin bincike game da daukar ma'aikatan yan sanda. 


Marubuci ©Ahmed El-rufai Idris

0 Response to "Neman Aikin 'Yan Sanda Hukumar ta Saki Sabuwar Sanarwa"

Post a Comment