--
Rancen Kudi marar Kudin Ruwa: Jama'a muyi hattara,  Kada Bamuci Kudiba, Biyan Kudi Ya Kamamu,  Duba Wasu Kusakurai Da Mutanen mu Keyi Akan Karbar Kaya Daga Gurin Vendors Yau Nirsal Ta Fitar Da Sabuwar Sanarwa

Rancen Kudi marar Kudin Ruwa: Jama'a muyi hattara, Kada Bamuci Kudiba, Biyan Kudi Ya Kamamu, Duba Wasu Kusakurai Da Mutanen mu Keyi Akan Karbar Kaya Daga Gurin Vendors Yau Nirsal Ta Fitar Da Sabuwar Sanarwa





Masu bibiyarmu barkanmu da yau,  Muna fatan kuna cikin koshin Lafiya, yau mun zabi mu danyi Rubutu Kadan Domin Ankarar Da Mafiya Yawan Al-ummah Masu Cin Gajiyar Rancen Kudi Da Gwamnatin Tarayyar Najeriya Ke Bayarwa Ga 'Yan Najeriya, wanda akayiwa Lakabi Da Rance Wanda Ba Kudin Ruwa Acikinsa,  



Abinda Muka Hango Kuma Muke Jiyewa Al-ummah Tsoro Shine Kada Mutum Yaje Garin Neman Gira Yazo Ya Rasa Ido Gaba Daya,  Abinda Muke Nufi Anan Shine Kada Kaje Domin Neman Karbar Kaya Ka Ansarwa Wani Yabarka Da Biyan Kudi,  Domin Su Wadan nan kudin ba kyauta Baneba,  Rance Ne Kuma Duk Wanda Aka Bawa Sai Yabiya, 


Matsalar Da Muka Hango Itace Nirsal Sun Banbanta Mai Neman Lamunin Kudi Da Vendor Misali Kana Kano Sai Ace Maka Vendor Naka yana Abuja Ko Lagos Ko Wata Jaha Daban Wadda Ba Taka ba,  


Vendor Din Suna Aikawa Masu Karbar Kaya Ko Kudi Email Da Cewa Suyi Download Na Wani Form Su Cika Da Full Sun,  BVN,  Sahannu,  Dadai Sauran Abubuwan Da Zasu Tabbatar Da Cewa Kaine Kuma Ka Amince Da Dukkan Abinda Ke Ciki, Ciki Kuwa Harda cewa Ka Anshi Kayanka,  



To Tabbas Yayin Daka Aika Wannan Bayanan Kasani Tamkar Ka  anshi kayanka Ne Ko Kudinka,  Kuma Wallahi Indai Har Baka Anshi Kayan ba,  Biya Ya Hauka Wani Ya Karba Anbarka Da Biya,  


Don Haka Muke Bawa Mutanen Mu Shawara Dasu Bude Idanunsu Sosai Su Fuskanci Duk Wani Vendor Ko A Ina Yake Kada Ku Yarda Da Maganar Email Ko WhatsApp Kuje Ku Sameshi Ayita Ta Kare Nan Take Babu Maganar Tura Bayanai Ta Wata Hanya Daban,  


Yin Hakan Na Iya Zama Ganganci Sosai Kuyi Share Ga Sauran Al-ummah Domin Susan Halin Da Ake Ciki, 

0 Response to "Rancen Kudi marar Kudin Ruwa: Jama'a muyi hattara, Kada Bamuci Kudiba, Biyan Kudi Ya Kamamu, Duba Wasu Kusakurai Da Mutanen mu Keyi Akan Karbar Kaya Daga Gurin Vendors Yau Nirsal Ta Fitar Da Sabuwar Sanarwa"

Post a Comment