--
Yadda zakuyi cancel auto renew na data a layin MTN cikin sauki

Yadda zakuyi cancel auto renew na data a layin MTN cikin sauki



Barka da zuwa Wannan cibiya mai albarka wacce take wayar da kan al'umma game da Internet da social media, kuci gaba da kasancewa damu zaku ji dadi


Yau kuma mun zo muke ne da yadda ake cancel na data auto renew a layin MTN, kafin mu tafi bayani gadan-gadan ya kamata musan menene data auto renew.


Menene MTN data auto renew?


MTN Data auto renew tsari ne Wanda MTN suka bullo dashi Wanda da zaran ka sayi data a layin su idan kasa kudi bayan karewan subscription na datan da kayi nan take zasu cire kudin su turo maka data, a takaice Wannan shine ma'anar data auto renew.


Mutane da dama basu San yadda ake tsayar da Wannan tsari ba, Wannan shine babban dalilin yin Wannan bayani don sanar da wadanda basu sani ba a kyauta ba tare da na data ba.


Duk lokacin da ka sayi data Akwai bukatan ka tsayar da auto renew, idan ba kayi hakan ba bayan karewan wa'adin subscription da kayi datan zai sake sayuwa da kan shi.

Yadda ake dakatar da auto renewal na data a layin MTN

Kamar yadda tsarin sayan data yake da yawa haka ma yadda ake dakatar da auto renewal yake, yadda ake dakatar da na kullum daban yake da yadda ake tsayar da na kwana biyu ko sati daya da sauran su.


Yadda zaka dakatar da auto renew na subscription a rana (daily)

Na 50MB a rana — Tura "NO104" zuwa 131
Na 150MB a Rana —Tura  "NO113" Zuwa 131

 

Wannan shine yadda ake tsayar da auto renewal na kullum a layin MTN (MTN daily plan).

Yadda zaka tsayar da MTN auto renew na sati-sati (weekly)

Na 150MB a sati — Tura "NO102" Zuwa 131
Na 500MB a sayi — Tura "NO103" Zuwa 131

Wannan sune kadan daga cikin tsarin MTN na fita (optout) daga auto renewal, mafi yawan lokuta idan a ka sayi data suna turo sakon yadda ake fita sai ka fita saboda gudun baka shirya sayan data ba ka sayi na dole.


SOURCE: LAMBUN SADARWA

0 Response to "Yadda zakuyi cancel auto renew na data a layin MTN cikin sauki "

Post a Comment